Kwastam ta samu kudin da suka zarce abin da aka daurawa Hameed Ali ya yi a shekarar nan

Kwastam ta samu kudin da suka zarce abin da aka daurawa Hameed Ali ya yi a shekarar nan

  • Hukumar kwastam mai yaki da fasa-kauri ta bayyana adadin kudin da ta zuba a asusun tarayya a 2021
  • A wajen wani taro da aka yi a Apapa, Timi Bomodi ya shaidawa ‘yan jarida NCS ta iya samun N2.3tr
  • Bomodi yace wannan kudi ya haura abin da gwamnati ta ci buri daga kwastam da Naira biliyan 600

FCT, Abuja - Hukumar kwastam mai yaki da fasa-kauri a Najeriya, ta bayyana cewa ta samu sama da Naira tiriliyan 2.3 a cikin wannan shekarar ta 2021.

Jaridar Daily Trust ta rahoto wani babban jami’in kwastam na kasa, Timi Bomodi ya na wannan jawabi a jiya, ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021.

Timi Bomodi ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da hukumar kwastam ta kira da ‘yan jarida sauran masu ruwa da tsaki a Apapa, a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

A cewar mataimakin jami’in yada labarai da hulda da jama’a na kwastam, an samu wadannan kudi ne daga watan Junairu zuwa 19 ga watan Disamba, 2021.

Mun samu karin fiye da N600bn - NCS

Kamar yadda Newswire ta bayyana, an ji Bomodi yana cewa wadannan kudi da aka samu, sun haura hasashen da aka yi na samun Naira tiriliyan N1.687.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwastam
Manyan jami'an kwastam Hoto: @nigeriacustomsauctionsales
Asali: Facebook

Mafi yawan kudin-shigan da kwastam ta samu ya fito ne daga tashar Apapa da Tin-Can Island.

“Zan iya tabbatar maku da cewa mun samu sama da Naira tiriliyan 2.3, ma’ana mun samu abin da ya wuce harinmu na Naira tiriliyan N1.687 a 2021.”
“Bayan nasarar da muka samu a 2020, sai aka ba kwastam nauyin tatso N1.679tr a asusun tarayya. Ana sa ran a daura a kan rufe iyakoki da aka yi.”

Kara karanta wannan

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

- Timi Bomodi

Rufe iyakokin da gwamnati tayi

Da yake bayanin hikimar rufe iyakokin kasar, Timi Bomodi yace gwamnatin tarayya tayi wannan ne domin hana shigowar kananan makamai cikin Najeriya.

Hakan kuma zai rage matsalar fasa-kauri da shigo da miyagun kayan da gwamnati ta haramta.

Rashin tsaro zai iya zama tarihi a wata 6?

Dazu aka ji tsohon Minista, Mohammed Magoro ya na ganin babu abin da zai hana a kawo karshen matsalar tsaro a watanni 6 kamar yadda aka yi a baya.

Janar Mohammed Magoro ya bada shawarwari, sannan ya fadi kasashen da ya kamata Gwamnatin Najeriya ta hada-kai da su domin samun kayan yaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng