Shugabannin kungiyar ASUU sun dauki matsaya a kan batun sake komawa yajin aiki a Najeriya
- Kungiyar ASUU ta yi zama domin ta duba yiwuwar sake shiga wani yajin-aikin a jami’o’in Najeriya
- Shugabannin ASUU na kasa sun cin ma matsaya bayan taron NEC da aka gudanar a jami’ar UNIABUJA
Shugaban ASUU na kasa, yace gwamnati ta gagara cika alkawuranta, amma an dakatar da shiga yajin-aiki
Abuja - Kamar yadda jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba, 2021, kungiyar ASUU tayi wani zama a birnin tarayya Abuja.
Shugabannin ASUU na kasa sun yi wannan zama a jami’ar tarayya ta Abuja, inda suka tattauna a game da matsayar da za su dauka a kan gwamnatin tarayya.
Bayan wannan zama sai aka ji matsayar da aka cin ma shi ne babu maganar zuwa yajin-aiki a wannan lokaci, amma ASUU na cigaba da tuntubar malamai.
Kungiyar ASUU ta bada wannan sanarwa a wani jawabi da shugabanta na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya fitar. Legit.ng ta samu wannan takarda.
Farfesa Osodeke ya yi wa takardar da ya ba ‘yan jarida take da ‘Enough of blackmail’, inda ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin batawa malaman jami’a suna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkawuran da aka yi mana - ASUU
Shugaban kungiyar ta ASUU ya ce gwamnatin tarayya ta yi watsi da alkawarin kafa kwamiti da za su sake duba yarjejeniyar da aka sa wa hannu a shekarar 2009.
Baya ga batun alawus din da za a ba malamai, ASUU tace an yi alkawari da gwamnatin tarayya cewa NUC za ta duba maganar yawa kafa jami’o’in jiha da ake yi.
Kungiyar ta zargi gwamnoni da yawan bude sababbin jami’o’i a lokacin da ba a iya daukar dawainiyar sauran jami’o’in da ake da su a yanzu haka da kyau.
Punch tace sauran alkawuran da ASUU ta ke zargin gwamnati ta saba sun hada da watsi da manhajar IPPIS wajen biyan ta albashinta, a komawa tsarin UTAS.
Ragowar sun hada da biyan bashin kudin karin girman da malamai suke bin gwamnatin tarayya.
ASUU: Matakin da aka dauka a yanzu
“NEC ta tabbatar da cewa gwamnati ta gaza cika wadannan alkawura da aka yi a yarjejeniyar FG-ASUU na 2009 da sauran MoU da MoA.”
“La’akari da tattaunawa da kokarin sulhu da ake yi, NEC ta dauki matakin sake duba lamarin nan gaba, da niyyar daukar matsaya.” – Emmanuel Osodeke.
Wa'adi ya wuce, gwamnati ba ta yi komai ba
A kwanakin baya an ji cewa kungiyar ASUU ta ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zuwa karshen watan Agustan 2021, ta tuntube ta ko a sake rufe jami’o’i.
Har wannan wa’adi na kwanaki 21 suka shude, ba a iya biyawa malaman jami'an bukatun na su ba.
Asali: Legit.ng