Karshen shekara: Gwamnan APC zai ba duka ma’aikatan jiharsa alawus domin su shana

Karshen shekara: Gwamnan APC zai ba duka ma’aikatan jiharsa alawus domin su shana

  • Gwamnatin jihar Legas za ta biya duk wani ma’aikacin jihar alawus na karshen shekarar nan ta 2021
  • Ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta za su samu 30% na albashinsu a Disamba
  • Gwamna Babajide Sanwo Olu ya bayyana haka a wata sanarwa da ta fito daga Hakeem Muri-Okunola

Lagos - Gwamnatin jihar Legas ta bada sanarwar rabawa ma’aikatan gwamnati alawus na bikin karshen shekara.

Shugaban ma’aikatan gwamnatin Legas, Hakeem Muri-Okunola ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar.

Takardar sanarwar ta shiga hannun mataimakin gwamna, shugaban majalisar dokoki, da kuma sakataren gwamnati.

The Eagle tace an sanar da kwamishinoni, hadimai da shugaban ma’aikatan gidan gwamna a kan wannan cigaba.

Sanarwar tace Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya amince a biya ma’aikata 30% na albashin da suke karba duk wata.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

Gwamnan APC
Gwamna Babajide Sanwo Olu cikin talakawa Hoto: @jidesanwooluofficial
Asali: Facebook

Su wa za su amfana da wannan kudi?

Jaridar tace kyautar ta shafi mukarraban ‘yan siyasa, ma’aikatan kananan hukumomi, hukumar SUBEB da dakarun LNSC.

Wani abin ban sha’awa game da wannan kyauta da gwamnati za ta bada shi ne ba za a cire haraji a kan wannan kudi ba.

Sanarwar shugaban ma'aikatan gwamnati

“Ma’aikatan gwamnati su san za a biya su 30% na albashinsu a matsayin kyautan karshen shekara.”
“Za a biya kudin ne tare da albashin watan Disamban 2021, kuma haraji ba zai hau kan su ba.”
“Ana ganin ma’aikata za su fi dagewa wajen aikinsu domin manufofin gwamna su tabbata.”
“Duk wasu shugabannin ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su dauki mataki.”

- Hakeem Muri-Okunola

ASUU ta maidawa 'Yan majalisa martani

Kara karanta wannan

Tsaro: Kungiyar Izala ta yi kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu'a

Shugaban ASUU na reshen Legas, ya bayyana cewa Gwamnatin APC ta sa Malamai sun zama Direbobi da Manoma saboda wahalar rayuwa.

Dr. Adelaja Odukoya yace a lokacin da ake biyan ‘Yan Majalisa miliyoyin kudi duk wata, an bar malaman makaranta da yunwa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng