A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya 'yar shekara 20
1 - tsawon mintuna
Daura, jihar Katsina - Daily Nigerian na ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.
An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano.

Asali: Facebook
Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani gajeren bidiyo ya nuna yadda Amaryar ke tika rawa.
Kalli bidiyon:
Hakazalika rahoton yace Magajin Garin Daura ne ya wakilci Sarkin wajen bikin daurin auren.
Asali: Legit.ng
Tags: