Kwanan Nnamdi Kanu 3 bai ci abinci ba, Kungiyar IPOB ta laburta

Kwanan Nnamdi Kanu 3 bai ci abinci ba, Kungiyar IPOB ta laburta

  • Karo na biyu, Nnamdi Kanu na ikirarin ba'a bashi abinci a hannun hukumar DSS da yake tsare
  • Kungiyar IPOB ta ce kasashen waje su kawo wa Nnamdi Kanu dauki
  • Kotu ta baiwa DSS umurni ta bari Nnamdi Kanu yayi duk walwalan da yake so

Kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB a ranar Asabar ta bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya DSS ta hana shugabanta, Nnamdi Kanu, abinci tsawon kwanaki uku yanzu.

IPOB ta bayyana hakan a jawabin da Kakakinta, Emma Powerful, ya saki inda ya bukaci gwamnati ta kai Kanu Kurkuku maimakon wahalan da yake sha hannun DSS.

Kungiyar ta ce tana son duniya ta sani cewa gwamnati na cin zarafin shugabanta Nnamdi Kanu, PM News ta ruwaito.

Yace:

"Hukumar DSS tana amfani da yunwa wajen kokarin halaka shugabanmu, Nnamdi Kanu. Sun cigaba da tsareshi cikin hali mai wuya tun lokacin da aka dawo da shi Najeriya a Yuni."

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana

"Su kai shi kurkukun Kuje kawai kafin ya bayyana a kotu."
"DSS ta hana shugabanmu, Mazi Nnamdu Kanu abinci tsawon kwanaki uku zuwa hudu yanzu."

Kwanan Nnamdi Kanu 3 bai ci abinci ba, Kungiyar IPOB ta laburta
Kwanan Nnamdi Kanu 3 bai ci abinci ba, Kungiyar IPOB ta laburta

Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana

A farkon makon nan, Lauyan Shugaban kungiyar masu neman kafa kasar Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu, mai suna Ifeanyi Ejiofor ya koka kan yadda ake wahalar da shi a kurkukun hukumar DSS.

A jawabin da ya saki ranar Talata, Ejiofor ya bayyana cewa DSS bata bi umurnin da kotu ta bata makon da ya gabata ba.

Za ku tuna cewa a zaman kotu da akayi makon da ya gabata, Mai Shari'a Binta Nyako ta amsa bukatu biyar da lauyoyin Kanu suka gabatar.

A cewar Ifeanyi Ejiofor sun shiga duba Nnamdi Kanu ranar Litinin, 6 ga Disamba don ganin halin da yake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: