Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

  • Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega ya tona yadda Alkalai su ke samun kazaman kudi da shari'a
  • Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa Alkalai su na saida shari’a a kotu ga duk wanda ya fi dukiya
  • Malamin jami’ar yace sauraron karar zabe ya na cikin hanyar da Alkalai su ke tara makudan kudi

Ibadan - Tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega yace wasu mara gurbin Alkalai su na cikin masu kawo cikas.

Jaridar Punch ta rahoto Farfesa Attahiru Jega yana cewa ana sa Alkalan kotu a harkar sauraron korafin zabe ne domin su samu hanyar da za su cika aljihunsu.

A cewar babban malamin jami’ar, wasu Alkalan su na saida shari’ar zabe, sai suyi wuf, suyi ritaya daga aiki domin gudun majalisar shari’a ta NJC ta hukunta su.

Kara karanta wannan

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Farfesan ya yi wannan fallasa a lokacin da ya gabatar da watta lacca domin tunawa da Owolabi Afuye da kungiyar lauyoyi ta NBA ta shirya a Ibadan, jihar Oyo.

Bikin makon shari'a a Ibadan

Kamar yadda jaridar ta rahoto a ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, NBA ta shirya wannan zama ne yayin da ake bikin ranar shari’a ta Duniya a makon nan.

Farfesa Jega
Farfesa Attahiru Jega Hoto: www.cfr.org
Asali: UGC

A jawabin na sa, tsohon shugaban jami’ar ta Bayero da ke garin Kano, yace danyen aikin da Alkalai suke yi yana cikin abubuwan da ke haddasa rashin tsaro.

Jawabin Farfesa Attahiru Jega

“Wasu manyan lauyoyi sun yi kazamin kudi a dalilin kare jami’an gwamnati marasa a kotu, ko ta kare ‘yan siyasa a shari’ar zaben gwamnoni da shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

“Haka zalika Alkalai da-dama sun yi kaurin-suna wajen cin haram ta hanyar karbar kudi domin su saida shari’a, musamman a shari’ar sauraron korafin zabe.”
“A baya ana zaben tsofaffin Alkalan da suka kusa yin ritaya a matsayin wadanda za su saurari karar zabe, su kuma sai su saida shari’ar ga wanda ya fi kudi.”
“Sai su samu kudi, su yi maza su yi ritaya domin su kubuta daga hukuncin majalisar NJC.” – Jega.

EFCC na rigima da NBA

A makon nan aka ji cewa kungiyar NBA ta na barazana saboda yadda wasu jami’an EFCC su ka cafke Lauya a tsakiyar kotu bayan an kammala zaman shari'a a kotu.

Dawood Ajetunmobi ya fitar da sanarwa a madadin kungiyar NBA, yace an kama Temitope Oyedipe esq. EFCC ta tabbatar da cewa lallai wannan lauya na hannunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng