Nasara: Sojoji sun aika mayakan Boko Haram/ISWAP lahira a wani harin kwantan bauna a Borno
- Rundunar sojin Operation Hadin Kai dake aiki a arewa maso gabas na cigaba da samun nasara kan yan ta'addan Boko Haram da ISWAP
- A wata sanarwa da rundunar sojin kasa ta fitar ranar Alhamis, tace sojin OHK sun yi wa wasu yan ta'addan Boko Haram kwantan Bauna a Borno
- COAS Farouk Yahaya, ya yaba da namijin kokari da jajircewar sojojin, tare da rokon su cigaba da irin haka
Borno - Dakarun sojin Operation Hadin Kai na sashi na 1, sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP guda uku a jihar Borno ranar Laraba.
Sojojin sun samu wannan nasara ne bayan sun yi wa yan ta'addan kwantan ɓauna a ɗaya daga cikin sanannun hanyar wucewan su dake kusa da hanyar Kwadal-Agapalwa-Amuda.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin kasa ta fitar a shafinta na Facebook ranar Alhamis, ɗauke da sa hannun kakakinta, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.

Kara karanta wannan
Jirgin yakin NAF ya yi ruwan wuta kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja, ya kashe 45

Source: Facebook
Sanarwan tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Dakarun sojin waɗan da suka fito sintiri yankunan Agapalwa da Amuda, sun samu labarin ayyukan yan ta'adda, hakan yasa suka jira su a hanyar da suke wucewa."
"A musayar wutar da suka yi tsakani, sojojin sun musu luguden harsasai, wanda yasa da yawa suka hallaka. Bayan haka sojin sun kwato Mashine Gun ɗaya, gurneti uku, alburusai 62, mashin ɗaya, da keke uku daga hannun yan ta'addan."
"A halin yanzun dakarun sojin na cigaba da bin sawun yan ta'addan domin tsaftace yankin daga yan ta'addan da suka tsere a gwabzawar."
COAS ya yaba wa Sojojin
Kakakin rundunar sojin ƙasa ya bayyana cewa shugaban sojoji, Janar Farouƙ Yahaya, ya yaba da namijin kokari da jajircewar da jami'an sojin suka nuna.
Haka nan kuma hafsan sojin ya roki su cigaba da matsa lamba har su samu nasarar yakin da suke da yan ta'adda.
A wani labarin kuma Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja
Jirgin yakin rundunar sojin sama (NAF) ya kashe yan bindiga sama da 45 a wani hari da ya kai maɓoyarsu kan hanyar Kaduna-Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa luguden wutan saman ya rushe gidan wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a yankin.
Asali: Legit.ng
