An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

  • Kungiyar Gobir Development Association ta sake rubuta wata wasika zuwa ga shugaban Najeriya
  • Dattawan na Sokoto sun bayyanawa Muhammadu Buhari yadda ake yi masu kisan gilla a kauyuka
  • An sanar da shugaban kasa cewa mayakan Bello Turji sun tasa mutane a gaba, su na yi masu ta’adi

Sokoto - Manyan mutanen garin Sabon Birni a karkashin kungiyar Gobir Development Association sun aikawa shugaba Muhammadu Buhari takarda.

Jaridar Daily Trust tace kungiyar Gobir Development Association ta sanar da mai girma shugaban kasa ne irin kisan kiyashin da ake yi wa mutanen Sabon Birni.

A wasikar ta su, dattawan jihar sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi, babu wani katabus a tare da su, bayan zaluncin da aka yi masu kamar dai yadda aka saba.

Da suke bayani a takardar a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, kungiyar tace yan bindiga sun addabi yankin Isa, Sabon Birni da Goronyo da bangaren Shinkafi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

Buhari
Buhari da wasu manyan kasa Hoto: GarShehu
Asali: Facebook

“’Yan bindiga su na kai wa wadannan mutane hari a duk ranar Duniya. Shahararren ‘dan bindiga, Bello Turji da mutanensa su na ta’adi yadda suka ga dama; su yi kisa, su yi fyade, su yanka mutanenmu, su hana su neman abinci, ba tare da wani dalili ba.”
“Kama-karyarsu ta kai inda ta kai, har su na ayyana kansu a matsayin shugabanni, su na karbe duk abin da suka ga dama daga hannun mutane." - Kungiya

Kamar yadda rahoton ya bayyana, dattawan sun ce wadannan ‘yan bindiga su na karbar kudi da sunan haraji, da kayan abinci, magunguna, har da matan mutane.

“Ran ka ya dade, a baya mun kawo maka irin wannan kuka bayan abin da ya faru a Garki, kilomita biyar da Sabon Birni, inda aka kashe mutum 80 a dare daya.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

“A wancan lokaci, mun razana har ta kai mun gagara birne gawawwakin saboda tsoron wadannan ‘yan ta’adda su sake dawo mana, su kashe mu.” – Kungiya.

Gobir Development Association tace babu abin da ake gani a Gajit, Lajinge, Tarah, Unguwar Lalle, Kurawa, Gangara, da Garin Idi sai hayaki da jinanen Bayin Allah.

An kona mutane a cikin mota

Wannan wasika ta fito ne jim kadan bayan ‘yan bindiga sun tare wata mota da ta dauko fasinjoji a kauyen Gidan Bawa, suka sa mata wuta, sai da kowa ya mutu.

Daga baya an ji rundunar 'yan sandan Najeriya na reshen Jihar Sokoto sun tabbatar da mutuwar mutane 23 a harin da 'yan bindiga suka kai wa matafiyan a jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng