Lauyoyi za su yi rigima da EFCC a dalilin damke abokin aikinsu da ake je aka yi a kotu

Lauyoyi za su yi rigima da EFCC a dalilin damke abokin aikinsu da ake je aka yi a kotu

  • Kungiyar NBA ta lauyoyi na reshen garin Osogbo ta zargi EFCC da kama mata wani lauyanta a Osun
  • Sakataren yada labarai na kungiyar yace har cikin kotu aka tura jami’an EFCC suka kama lauyan
  • Dawood Ajetunmobi ya fitar da sanarwa da yawun NBA a kan abin da ya faru da Temitope Oyedipe

Osun - Shugabannin kungiyar lauyoyi na garin Osogbo, a jihar Osun su na barazanar yin ta, ta kare da hukumar EFCC saboda kama masu abokin aiki.

Punch ta fitar da rahoto a safiyar Alhamis cewa kungiyar NBA ta koka a kan abin da ya faru da wani lauya a jiya, ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021.

Sakataren yada labarai na NBA na reshen Osogbo, Dawood Ajetunmobi esq yace jami’an EFCC sun shigo har cikin kotu sun damke Temitope Oyedipe esq.

Kara karanta wannan

'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

NBA tace wadannan jami’ai na hukumar EFCC da suka zo daga Legas sun kutsa kai cikin babban kotun jihar Osun da ke garin Ile-Ife, suka yi gaba da lauyan.

A sanarwar da Dawood Ajetunmobi ya fitar da yawun bakin kungiyar, yace an kama Oyedipe ne bayan an gama zaman kotu inji Jaridar nan ta Daily Post.

Lauyoyi
Wasu Lauyoyi a kotu Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Jawabin da NBA ta fitar

“Nan-take labarin ya isa kunnen kwamitin kare hakkin Bil Adama na kungiyar NBA na reshen Osogbo, aka tattauna a kai.”
“Kuma aka zabi lauya, Nurudeen Kareem ya je ofishin na hukumar EFCC da ke Legas.”
“Shugaban kungiya na reshen, Hassan Agbelekale, ya kuma tuntubi takwarorinsu da ke Legas da Ikeja domin a san yadda za ayi maza a fito da lauyan.”

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

“Da kwamitin ya tuntubi EFCC a waya, sai aka tabbatar cewa babu shakka an kama Oyedupe bayan ya gaza bayani a kan shari’ar da yake karewa.” – NBA.

Rahoton yace kungiyar ta NBA ta na kokarin fadakar da sauran abokan aikinta da ke fadin Najeriya game da wannan batu domin a gaggauta fito da lauyan na ta.

A ba Sowore wayarsa da karin N2m - Kotu

Ku na da labari cewa a shekarar 2019 da aka kama Omoyele Sowore, jami’an DSS sun karbe waya da kudi har N10, 000 da aka samu a hannunsa a wancan lokacin.

'Dan gwagwarmayar ya kalubalanci karbe masa wayar da aka yi a kotu, kuma ya yi nasara inda Alkali tace a biya shi N2m saboda hukumar DSS ba ta bi doka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng