Shugaban kasa ya yabi Minista yayin da ya cika shekara 70, ya jinjinawa irin kokarinsa

Shugaban kasa ya yabi Minista yayin da ya cika shekara 70, ya jinjinawa irin kokarinsa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya yabi Alhaji Lai Mohammed bayan ya cika shekara 70 da haihuwa
  • Mai girma shugaban kasa ya fitar da sakon taya murna ne ta bakin hadiminsa, Femi Adesina a jiya
  • Buhari yace Ministan ya taimaka wajen kawo canjin gwamnati lokacin da yake da mukami a APC

Abuja - A ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed.

Mai girma shugaban kasar ya yabi Ministan ne domin taya shi murnar cika shekara 70 a Duniya.

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar a birnin tarayya Abuja, ya taya Ministan zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya taya ministansa murnan cika shekaru 70

Adesina ya yi wa sakon shugaban kasa take da ‘President Buhari hails Lai Mohammed at 70’, watau shugaban kasa ya jinjinawa Lai Mohammed a shekara 70.

Jawabin Femi Adesina

“Shugaban kasa ya na taya Ministan murnar kai wannan munzali, ya shafe shekaru masu yawa wajen bautawa kasar nan.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi aiki a matsayin lauya da ‘dan kasuwa, kafin ya shiga siyasa inda ya zama shugaban ma’aikatan gwamnan Legas.”
Shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: femi.adesina
Asali: Facebook

“Daga nan ya zama sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa.” – Muhammadu Buhari.

A cewar Muhammadu Buhari, Lai ya bada gudumuwa sosai a jam’iyyar APC wajen hada rundanar sojojin baka da suka taimaka wajen kawo sauyin gwamnati.

Shugaban kasar ya yabawa Ministan a kan irin kokarin da yake yi dare-da-rana wajen fahimtar da al’umma da jawowa Najeriya farin jini, tare da yada labarai.

Kara karanta wannan

Daga dawowar Buhari, Shima Osinbajo ya shilla Dubai don halartan taron iskar Gas na girki LPG

“Buhari ya bi sahun ‘yan majalisar zartarwa da jam’iyyar APC da ‘yan jarida wajen taya Ministan murna da fatan karin lafiya da nisan kwana.” – Adesina.

Rikicin APC a Kano

A baya kun ji yadda rigimar cikin gidan APC ta canza salo bayan uwar jam’iyya ta nuna ta na tare da tsagin su Abdullahi Abbas ne ba su Amadu Danzago ba.

A game da rikicikin da aka yi a jihar Kano, hedikwatar jam'iyyar APC tace ba ta san da zaman nasarar da ‘Yan G7 suka samu a kan tsagin Ganduje a Kotu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng