Shugaban kungiyar ASUU ya bayyana inda aka kwana a kan yiwuwar komawa yajin-aiki
- Malaman Jami’a sun yi karin haske a game da shirin sake rufe makarantun jami'o'i kwanan nan
- Shugaban Kungiyar ASUU yace za su dauki mataki ne bayan sun gama tattaunawa da rassan jami’o’i
- Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Oshodeke yace har yau ba su ji daga bangaren gwamnati ba
Kungiyar ASUU ta malaman da ke koyarwa a jami’o’i tace ta na sauraron rahoto daga sauran rassanta kafin ta dauki mataki a kan zuwa yajin-aiki.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta gagara cika alkawuran da ta yi wa kungiyar ASUU.
Jaridar Punch tace ta yi magana da shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Oshodeke, a ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021 a kan matakin da za a dauka.
Farfesa Emmanuel Oshodeke ya shaidawa ‘yan jarida sai sun ji matsayar ‘ya ‘yan kungiya da ke reshen sauran jami’o’in kasar nan kafin su dauki mataki.
A cewar Farfesa Oshodeke, tun da wa’adin da suka bada ya cika a ranar Lahadin da ta wuce, har yanzu ba su ji ko uffan daga bangaren gwamnatin tarayya ba.
Abin da shugaban ASUU ya fada
“Mun gama babban taronmu, kuma mun komawa sauran rassoshinmu. Rassanmu za su fada mana abin da za mu yi a gaba.”
“Ba mu ce mun bada wa’adin sa’o’i 24 ba, abin da mu ka ce shi ne za mu tuntubi ‘ya ‘yan kungiyarmu nan da sa’o'i 24.”
“Mun ba su kwanaki 10 zuwa mako biyu su dawo gare mu, sai mu tattauna a kan abubuwan da ya kamata mu yi.” – Oshodeke.
Ina labarin gwamnatin tarayya?
A cewar Oshodeke, har yanzu kungiyar ASUU ba ta ji daga gwamnatin tarayya, a gwamnatance ba.
Legit.ng Hausa za ta cigaba da sauraron cigaban da ake samu a kan batun daga nan zuwa 20 ga watan Disamba, lokacin ake sa rai za a dauki mataki na gaba.
Abin da ke ci wa NUC tuwo a kwarya
A makon da ya gabata ne aka ji cewa hukumar nan ta NUC mai kula da jami’o’i a Najeriya ta koka a kan yawan jami’o’in bogin da suke aikin su a fadin kasar nan.
Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana wannan a wajen yaye daliban jami’ar Al-Hikmah a jihar Kwara inda ya samu wakilci wajen Farfesa Yahuza Bello.
Asali: Legit.ng