Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja

Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja

  • Jirgin yakin rundunar sojin sama (NAF) ya kashe yan bindiga sama da 45 a wani hari da ya kai maɓoyarsu kan hanyar Kaduna-Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa luguden wutan saman ya rushe gidan wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a yankin
  • Mazauna kauyukan dake yankin sun tabbatar da harin sojojin saman a yankin Rijana

Kaduna - Bayan samun tabbaci daga bayanan sirri, jirgin yaƙin sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai kan sansanin yan bindiga a yankin Rijana, dake kan hanyar Kaduna-Abuja.

Daily Nigerian tace harin sojojin sama ya yi raga-raga da wurin aje makamai da ginin gawurtaccen ɗan garkuwa, Ali Kwaja, kuma ya hallaka dandazon yan bindiga.

Yan bindigan na amfani da wannan wurin a matsayin maɓoyarsu, da kuma kaddamar da hari kan matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Jirgin yakin NAF
Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin jami'an soji ya shaida wa PRNigeria cewa harin da aka kai hanyar Kaduna-Abuja, shine ya tilasta matsa wa wajen binciken fasaha a hanyar.

Yace jami'an fasaha na rundunar soji sun gudanar da bincike kan hanyar, kuma suka gano motsin yan bindiga da maɓoyarsu.

Yadda jirgin ya kaddamar da harin

Jami'in yace:

"Yan bindigan dake kai mafi yawan hare-hare kan hanyar Kaduna-Abuja suna fitowa ne daga yankin Rijana-Kuzo."
"Bayan tabbatar da maɓoyar, sojojin sama na Operation Thunder Strike suka tashi jirgin yaki zuwa wurin abin harin. Lokacin da suka isa wurin sun hangi yan bindigan, sannan suka musu luguden wuta."
"Sojoji sun bi bayan wasu daga cikin yan bindigan da suka yi kokarin tserewa zuwa wani wurin, kusan kilomita 4 a kudancin Kaduna, inda suka karasa aika su lahira."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

Harin ya rushe gidan ƙasurgumin ɗan bindiga

Budu da ƙari, harin jirgin saman ya rushe gidan wani gawurtaccen dan bindiga a Kofita, bayan gano yan ta'addan na amfani da gidan wajen wasu ayyukan su.

Wasu mazauna kauyukan dake nesa da wurin, sun tabbatar da cewa yan bindiga aƙalla 45 harin sojin sama ya hallaka a yankin Rijana.

A wani labarin kuma Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara

A cewar wasu mazauna yankin, yan bindigan sun ce zasu cigaba da kai hari kauyuka har sai gwamnati ta buɗe kasuwar dabbobi ta Shinkafi.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan wani harin sojin sama da ya hallaka iyalan Turji, yan bindigan dake karkashinsa suka cigaba da matsawa mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262