Hukumar NUC ta bankado wasu jami’o’i da makarantun bogi 67 da ke bada satifiket
- NUC mai kula da jami’o’i a Najeriya ta koka a kan yawan jami’o’in bogin da suke aikin su a kasar nan
- Shugaban hukumar NUC na kasa, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed yace ana kokarin magance matsalar
- Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana wannan a wajen yaye daliban jami’ar Al-Hikmah a jihar Kwara
Kwara - Hukumar NUC mai kula da jami’o’in Najeriya ta bada sanarwar cewa ta gano wasu sababbin makarantu 67 na bogi da suke aiki a kasar nan.
Shugaban hukumar NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana wannan a lokacin bikin yaye daliban jami’ar Al-Hikmah, garin Ilorin, jihar Kwara.
Farfesa Abubakar Adamu Rasheed yace bayan haka,NUC ta na kokarin kirkiro tsarin da za a rika amfani da shi wajen auna kokarin manyan makarantu.
Jaridar The Abusites ta rahoto cewa shugaban jami’ar Bayero da ke garin Kano, Farfesa Yahuza Bello ya wakilci Abubakar Adamu Rasheed a wajen taron.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'o'i nawa ne a Najeriya?
“A halin yanzu, hukumar ta na kula da jami’o’in tarayya 43, na jiha 54 da na ‘yan kasuwa 99 a fadin Najeriya.”
Amma duk da sa idon da hukumar ta ke yi, Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana cewa su na fuskantar wasu kalubale, daga ciki akwai makarantun bogi.
“Wata matsalar da ake fama da ita ce jami’o’in bogi da makarantu da cibiyoyi da ake fama da su, wanda adadinsu ya kai 67 a kiyadar karshe da aka yi."
“Inda karin matsalar ta ke, duk jami’o’in su na bada satifiket.” - Abubakar Adamu Rasheed.
“NUC na daukar matakai ta hannun ma’aikatun gwamnati domin magance wannan matsala, musamman ta hanyar wayar da kan mutane a game da su.”
Farfesa Bello a madadin Abubakar Adamu Rasheed yake cewa za a yaki wannan matsala ne ta hanyar fitar da sunayen duk makarantun bogin da suke aiki.
Yajin aikin ASUU
A yau ku ka ji cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta gagara cika alkawuran da ta yi wa malaman jami’a tun da suka janye yajin-aiki a karshen 2021.
Wakilan gwamnati sun yi wa ASUU wasu alkawari kafin su yarda su koma aiki a 2020. Amma kawo yanzu malaman jami'an sun ce da sauran rina a kaba.
Asali: Legit.ng