Daya daga cikin malaman da suka yi Muqabala da Abduljabbar Kabara a Kano ya rasu
- Allah Ya yiwa malamin nan na Kano, Mas'ud Mas’ud Hotoro rasuwa a wani mummunan hadari
- Sheikh Mas'ud Hotoro ya rasu bayan motarsa tayi hadari daga Kaduna a hanyarsa ta zuwa Kano
- Malamin ne ya kalubalanci Abduljabbar Kabara daga bangaren Darikar Kadiriyyah a mukabala
Kano - A ranar Alhamis, 2 ga watan Disamba, 2021, Legit.ng Hausa ta samu labarin rasuwar babban malamin addinin musulunci, Sheikh Mas'ud Mas'ud Hotoro.
Rahotanni sun bayyana mana cewa Sheikh Mas'ud Mas'ud Hotoro ya rasu ne a sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Kaduna zuwa garin Zaria.
Malamai irinsu Jamilu Albanin Samaru Zaria sun tabbatar da wannan mummunan labari a yau da safe.
Da yake magana a shafinsa na Facebook, Albanin Samaru Zaria wanda ya na cikin hadiman gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya roki Allah ya jikan malamin.
Shehin malamin babban masanin Kur'ani ne, kuma ya shahara musamman ga mabiyar darikar Kadiriyyah. Hotoro kan gabatar da karatuttukan musulunci a Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Allah ya jikan mai bada kariya ga Annabi
“Allah Ya jikan Sheikh Mas'ud Mas'ud Hotoro. Daya Ne Cikin Malamai Masu Bada Kariya Idan An taba Jinibin Farin Jakada Annabimmu Muhammad Dan Abdullahi Tsira Da Aminci Su Kara Tabbata Agare Shi.”
Ya rasu Sakamakon Wani Mummunar Hadirin Mota. Allah Yajikansa Da Rahma Yasa Aljannah Makoma Gare Shi Damu Baki Daya Allahumma Ameen”
- Albani Samaru
Haka zalika kungiyar nan ta Munazzamatul Fityanul Islam Of Nigeria ta mabiya Darika sun tabbatar da wannan labari a kan shafinsu na Facebook dazu.
Wani Bawan Allah ya yi wa marigayin kirari da Garkuwan Annabi Muhammad (SAW). Shafin mu koma tsangaya suka ce Duniyar Al-Kur'ani tayi babban rashi.
Ana sa ran za ayi masa sallar jana'iza a gidansa da ke unguwar Hotoro, a garin Kano da kimanin karfe 2:00 na rana a gidan kamar yadda musulunci ya tanada.
Legit.ng Hausa ta na rokon Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannah ta zamo makoma a gareshi.
Asali: Legit.ng