Bayan hukuncin Kotu, Gwamnatin Ganduje ta kwace ofishin Lauyan tsohon Sarki Sanusi a Kano

Bayan hukuncin Kotu, Gwamnatin Ganduje ta kwace ofishin Lauyan tsohon Sarki Sanusi a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta garkame ofishin lauyan tsohon sarkin Kano bayan hukuncin da kotu ta yanke a Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'an gwamnatin Ganduje ne suka jagoranci rufe ofishin a Kano
  • Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) reshen jihar Kano, tace zata cigaba da bibiyar lamarin domin kare mambobinta da aikinsu

Kano - Kungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA) reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta samu labarin gwamnatin Kano ta kwace ofishin, Nureni Jimoh, SAN.

Sakataren NBA na jihar Kano, Haruna Saleh Zakariyya, a wata fira da Tribune Online ta gani, yace bayan sun samu bayani sun bincika don tabbatarwa.

Ganduje da Sanusi
Bayan hukuncin Kotu, Gwamnatin Ganduje ta kwace ofishin Lauyan tsohon Sarki Sanusi a Kano Hoto: everyday.ng
Asali: UGC

Punch ta rahoto Sakataren yace:

"Bayan samun wannan bayanan, ofishin kungiyar mu na Kano ya ɗauki mataki, ta hanyar tura mataimakin shugaba, Abbas Haladu, ya ziyarci wurin kasancewar shugaban baya gari."

Kara karanta wannan

Bayan Abinda Ya Faru, Gwamnatin Ganduje Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Ruwa a Bagwai

"A binciken da muka yi, mun tabbatar da cewa jami'an gwamnatin jihar Kano ne suka garkame ofishin."

Wane mataki NBA ta ɗauka?

Zakariyya yace kungiyar NBA zata cigaba da tuntuɓar ofishin Antoni Janar domin sanin ainihin dalilin ɗaukar wannan matakin da kuma inda aka kwana.

"Kungiyar lauyoyi reshen Kano zata cigaba da kokarin kare mambobinta, ayyukansu da kuma al'umma baki ɗaya."
"Zamu cigaba da sanar da mambobin mu halin da ake ciki kan lamarin yayin da muke cigaba da bincike, amma dai Malam Nureni SAN yana cikin koshin lafiya."

Ko meyasa gwamnatin Kano ta yi haka?

Matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka ba zai rasa alaƙa da hukuncin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke ba awanni 24 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

Kotun ta umarci gwamnatin Kano ta baiwa tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, hakuri kuma ta biya shi diyyar miliyan N10m bisa tsare shi da tauye masa hakki.

Nureni Jimoh SAN, shine ya jagoranci tawagar lauyoyin tsohon sarkin har suka samu nasara a shari'an, kuma hakan yasa aka rufe ofishinsa.

A wani labarin na daban kuma Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano

Ganduje ya roki matukan jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya har ya fi ƙarfinsa, domin rayuwar mutane ce a gaba.

Ya kuma yi addu'ar samun rahamar ubangiji ga waɗan da suka mutu, tare da fatan samun lafiya ga waɗan da ke kwance a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262