Mayakan ISWAP sun tarwatse yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano na shawagi a Buni Yadi

Mayakan ISWAP sun tarwatse yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano na shawagi a Buni Yadi

  • Sojoji na musamman sun dakile harin da yan ta'addan ISWAP suka yi yunkurin kaiwa kan mazauna garin Buni Yadi, jihar Yobe
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan ba su tsere ba duk da zuwan sojoji, inda suka fara zazzaafar musayar wuta a tsakanin su
  • Sai dai yan ta'addan sun nemi hanyar tsira yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano ya na shawagi a saman garin

Yobe - Dakarun soji na musamman Special Task na rundunar sojin kasar nan sun dakile yunkurin harin mayakan ISWAP kan jami'an tsaro da mazauna garin Buni Yadi.

Daily Nigerian tace an tura dakarun ne domin su fatattaki yan ta'addan ISWAP, waɗan da suka shiga garin Buni Yadi, wani babban gari a jihar Yobe, ranar Talata da yamma.

Super Tucano
Mayakan ISWAP sun tarwatse yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano na shawagi a Buni Yadi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar ta'addanci ISWAP sun shiga garin ne da misalin karfe 5:00 na yamma.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sace soja da fasinjoji 15 a Borno

Yan ta'addan sun samu damar kone ofishin yan sanda baki ɗaya, kafin sojoji su kawo ɗauki, inji wata majiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

PRNigeria ta rahoto cewa da farko yan ta'addan sun kekashe ƙasa, sun ki fita daga garin, duk da zuwan sojoji na musamman.

Yadda aka tarwatsa maharan

A cewar wata majiya daga cikin jami'an sashin fasaha, mayakan sun yi musayar wuta da sojojin mai zafi.

Yace:

"Amma sun yi kokarin tsira, inda suka arce lokacin da suka hangi sabon jirgin yakin sojojin sama Super Tucano ya fara shawagi a sararin sama."

Yan sanda sun kama yan bindiga 32

A wani labarin na daban kuma yan sanda sun cafke yan bindiga 32, sun kwato manyan makamai daga hannun su

Rundunar yan sandan ƙasar nan (NPF) ta damke wasu gawurtattun masu aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa, ayyukan yan bindiga da sauran su.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya yi ɓarin wuta kan yan ta'ddan Boko Haram da ISWAP a Gajiram

Kakakin yan sanda, Frank Mba, yace jami'ai sun samu nasarar cafke wasu daga cikin su ne a samamen da suka kai yankin Arewa ta yamma da ya haɗa da jihohin Zamfara , Sokoto, Kaduna, Kebbi da kuma Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262