Ba zamu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba, Farfesa Zulum

Ba zamu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba, Farfesa Zulum

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana yadda za'a yi da tyan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya
  • Zulum yace abinda ya kamata shine hukuntasu amma fa ba zasu yi hakan ba saboda wasu dalilai
  • Gwamnan ya ware kashi 64% na kasafin kudin 2022 wajen gina sabbin manyan ayyuka a jihar

Maiduguri - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa sam ba'a hukunta yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya ba.

Zulum ya ce idan aka hukuntasu, sauran yan ta'addan dake cikin daji ba zasu mika wuya ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda gabatar da kasafin kudin 2022 na jihar gaban majalisar dokokin Borno, rahoton Daily Trust.

Yace:

"Mambobin majalisa, muna bukatar hidayar Allah da kuma hikima domin kawo karshen rikicin da jiharmu ke fuskanta."

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

"Hukunta dukkan yan ta'adda ya dace muyi amma idan muka ce sai mun yi haka, zamu hana sauran masu son mika wuya su yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hakan na iya sa yan ta'addan su kara yawa, kuma wadanda ke karkara na iya fuskantan karin hare-hare."

Ba zamu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba, Farfesa Zulum
Ba zamu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba, Farfesa Zulum Hoto: Governor Of Borno State
Asali: Facebook

Tuban yan Boko Haram ikon Allah ne

Zulum yace mika wuyan da yan ta'addan keyi ikon Allah kuma dama ce na rage rikicin.

Ya kara da cewa amma ba zasu taba mancewa da halin da yan ta'addan suka jefa wadanda suka halakawa yan uwa kuma suka rasa muhallansu ba.

Yace:

"Ba zamu taba manta halin da wadanda aka kashewa yan uwa, suka rasa muhallansu, suka rasa rasa dukiyoyinsu ba."
"Wajibi ne mu bi hanyoyin samar da zaman lafiya kamar yadda aka shinfida shawari 16 a ranar 29 ga Agusta, 2021, inda muka tara manyan masu ruwa da tsaki, kuma aka yanke shawara kan tubabbun yan ta'adda."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: