NDLEA: Matar da aka cafke ta hadiyi ledoji 80 na Cocaine, ta yi kashin su a filin jirgi

NDLEA: Matar da aka cafke ta hadiyi ledoji 80 na Cocaine, ta yi kashin su a filin jirgi

  • Ma’aikatan NDLEA sun cafke wata mata da ta hadiye hodar iblis, za ta shiga kasar Saudi Arabiya
  • An yi ram da Adisa Afusat Olayinka ne a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
  • Adisa Olayinka tace ta yi wannan danyen aiki ne domin samun kudin da za ayi mata aiki a mahaifa

FCT, Abuja - Jami’an hukumar NDLEA da ke yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya, sun kama wata ‘yar kasuwa dauke da hodar iblis.

Gidan talabijin na TVC ya fitar da rahoto a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, 2021, cewa an kama Adisa Afusat Olayinka za ta je Saudi Arabiya.

Wannan Baiwar Allah, Adisa Afusat Olayinka mai shekara 46 ta na zama ne a Ibafa, jihar Ogun. Asalin ta mutumiyar garin Ilorin ce a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Rundunar soji ta kame jami'anta da suka ci zarafin wasu mazauna a yankin Abuja

Jami’an NDLEA sun yi nasarar cafke ta a ranar Asabar da ta wuce, ta na shirin shiga jirgin Qatar Airways a filin tashin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja.

Jaridar Punch ta ce daga nan aka wuce da ita zuwa ofishin hukumar NDLEA, inda tayi kashin ledoji 80 na hodar iblis daga ranar Laraba zuwa Lahadi.

NDLEA: Matar da aka kama
Adisa Afusat Olayinka Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda abin ya faru - Jami'in NDLEA

Daretan yada labarai da wayar da kai na NDLEA, Mista Femi Babafemi ya bayyana wannan a wani jawabi na musamman da ya fitar a Abuja a ranar Litinin.

“A hirar da aka rika da ita, wanda ake zargi ta bayyana cewa ta yi shekara guda ta na adana Naira miliyan 2.5 domin ta saye wadannan kwayoyi a hankAAli daga mutane a garin Akala, Mushin, jihar Legas.”
“Wanda ake zargi ta ce ta na saida tufafi ne, don haka sai da ta karbi aron N1m daga mutane uku domin ta hada kudin da za ta saye miyagun kwayoyi.” - Femi Babafemi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Babafemi yace wannan ‘yar kasuwa ta kashe wasu N1m domin sabunta fasfon fita waje, kuma ta mallaki takardar biza, da biyan kudin jirgin zuwa da dawowa.

Wannan mata ta ce ta na bukatar Naira miliyan bakwai ne domin ayi mata aikin IVF a mahaifa domin ta yi shekara 28 da aure, ba ta taba samun haihuwa ba.

Omicron a nahiyar Amurka

Kasar Kanada tace wasu mutane da su ka ziyarci Najeriya sun zo mata da Omicron. Ministan lafiya na Kanada, Jean-Yves Duclos ya bayyana haka a yau.

Jean-Yves Duclos ya bada sanarwar cewa an killace wasu mutane biyu masu dauke da sabon samfurin COVID-19 wanda aka fi sani da 'Omicron' a Ontario.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng