Yanzu-yanzu: Ranar Litinin zamu dawo da Sabis jihar Zamfara, Matawalle
1 - tsawon mintuna
Gusau - Gwamnan Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sanar da cewa ranar Litinin ko Talata za'a mayar da layukan sadarwa da aka kaste a jihar sakamakon matsalar tsaro.
Daily Trust ta ruwaito cewa Matawalle ya bayyana hakan ne yayin zaben Shugabannin jam'iyyar All Progressive Congress APC.
A taron, Gwamnan yace za'a sawo da sabis kuma mutane zasu koma cin kasuwanninsu na mako.
Zaku tuna cewa a ranar 4 ga Satumba an datse sabis domin shawo kan lamarin garkuwa da mutane da ya addabi jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"A bayanan da muka samu, an samu saukin hare-haren da ake kaiwa garuruwa kuma nan da Litinin ko Talata, kowa a jihar zai iya waya da jama'a."
"Muna daukan matakan tabbatar da cewa yan ta'adda sun sha wahala. Idan muan wahala, su ma su wahala."
Asali: Legit.ng
Tags: