Da Dumi-Dumi: Sarkin Tsaftar Kano, Alhaji Ja'afru Ahmad, ya rigamu gidan gaskiya
- Hadimin gwamnan jihar Kano kuma sarkin tsaftar Kano, Alhaji Jaafaru Ahmad Gwarzo, ya rigamu gidan gaskiya
- Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya a kasar Saudiyya
- Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jajantawa iyalan marigayin bisa wannan babban rashi
Kano - Rahoton da muke samu yanzun daga jihar Kano ya nuna cewa sarkin tsaftar Kano, Alhaji Ja'afaru Ahmad Gwarzo, ya rigamu gidan gaskiya.
Daya daga cikin yayan sarkin, Asma'u Ja'afaru Ahmad Gwarzo, ita ce ta tabbatar da rasuwar mahifin nata ga Freedom Radiyo.
Ta bayyana cewa mahaifin na ta ya rasu ne a kasar Saudiyya jim kaɗan bayan kammala masa aikin zuciya.
Kafin rasuwar Alhaji Ja'afaru Ahmad, shine babban mai baiwa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan tsaftar muhalli.
Da yake tabbatar da rashin, daya daga cikin iyalan marigayin, Alhaji Nasiru Sani Gwarzo, ya shaida wa manema labarai cewa Ja'afar Gwarzo yaje Saudiyya ne domin yin Umrah.
Tribune Online ta rahoto cewa Marigayi sarkin tsaftar Kano ya rasu ya bar mata da kuma ƴaƴa.
Ganduje ya yi ta'aziyya
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jajantawa iyalan marigayi, Alhaji Ja'afar Ahmad, bisa rasuwarsa.
Ganduje yace
"Rasuwar Alhaji Jaafar Ahmad Gwarzo, babban rashi ne gare mu, mun yi jimamin wannan babban rashin lokacin da labarin ya iske mu. Rasuwarsa ta bar wani babban giɓi."
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Abba Anwar, ya fitar ranar Laraba, kuma aka raba wa manema labarai.
Gwamnati da al'ummar Kano sun yi ta'aziyya
A sanarwan gwamna Ganduje yace:
"A madadin gwamnatin jihar Kano da al'ummar Kano, ina mai mika ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma masarautar Kano bisa wannan rashi. Allah ya gafarta masa, ya amshi kyawawan ayyukansa."
"A matsayinsa na sarkin tsaftar Kano ya damu matuka da inganta ɓangaren lafiya da tsafta a jihar Kano. Yanzu ya amsa kiran ubangiji, Allah ya masa rahama."
A wani labarin kuma Maganar Gwamna El-Rufa'i ta kada yan Najeriya su zabi PDP a 2023 ta bar baya da kura
Gwamnan Kaduna ya roki yan Najeriya musamman mutanen jihar kada su kuskura su zabi jam'iyyar PDP a 2023.
Sai dai wannan magana ba tai wa yan Najeriya dadi ba, inda tuni wasu suka fara sukar gwamnan.
Asali: Legit.ng