Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan kudin Janar Abacha da aka dawo da su a 2020
- An kai karar gwamnatin Muhammadu Buhari a kan yadda za ta batar da wasu Dala miliyan 300
- Gwamnatin tarayya tace za ta batar da kudin da aka karbo daga asusun Sani Abacha a kan ayyuka
- Kotu tayi watsi da karar da aka shigar, tace masu korafin ba su iya gabatar da wasu hujjojin kirki ba
Abuja - Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya da ke Abuja, Inyang Eden Ekwo, ya yi watsi da karar da aka shigar a kan AGF da gwamnatin tarayya.
The Nation tace kungiyoyi sun bukaci a sa idanu a kan yadda ake batar da wadannan makudan kudi.
PPP Advisories, cibiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre da Issa Shuaibu sun je kotu, suna so a sa ido a kan yadda ake kashe kudin satar Abacha.
Gwamnatin tarayya tayi ikirarin ta dawo da Dala miliyan 300 da aka samu a asusun tsohon shugaba, Marigayi Janar Sani Abacha wanda ya rasu a 1998.
Da yake zartar da hukunci a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, 2021, Inyang Eden Ekwo yace duk hujjojin da masu karar suka gabatar, ba su da wani karfi.
Kamar yadda The Guardian ta fitar da rahoto, Kotu tace hujjojin da ke gabanta, sun sabawa sassa na 102, 103, 104 da 105 na dokar kafa hujja ta shekarar 2011.
Mai shari’a Inyang Eden Ekwo yace wadanda suka shigar da kara ba su iya gamsar da kotu a kan karfin hujjojinsu ba, don haka ba zai karbe su a shari’ar ba.
Abin da ya jawo aka shiga kotu
A shekarar 2020 ne gwamnatin Muhammadu Buhari tayi nasarar dawo da wasu kudi da Sani Abacha ya sata, ta kuma ce za a kashe kudin ne a kan ayyuka.
Najeriya tace wadannan dala miliyan 300 za su tafi wajen karasa gadar Neja, fadada titin Abuja zuwa Kano da aikin babban titin Legas zuwa garin Ibadan.
PPP Advisories; CISLAC da Issa Shuaibu and co (PPP Advisories Consortium) ba su yarda da wannan matsaya da gwamnati ta dauka ba, sai suka je kotu.
A shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1449/2020, an yi karar AGF, ma’aikatar shari’a, Dayo Apata (SAN), hukumar BPP da kuma wasu manyan jami’a gwamnati.
Badakalar Mohammed Abacha
Kwanakin baya ne aka ji Mohammed Abacha ya fadawa kotu cewa ya yi amfani da sunan Mohammed Sani ne domin mallakar rijiyar man OPL 245.
Babban yaron tsohon shugaba Sani Abacha ya bayyana haka ne da aka wata shari’a da shi a kotu.
Asali: Legit.ng