Wani mutumi ya sayi gida da kudi N60m da aka tura masa cikin kuskure, yanzu Banki yace ya dawo da kudin
- Wani mutumi mai suna Russell Alexander ya sayi gida da kudi £110,000 (N60.7 million) da aka tura masa cikin kuskure
- Mutumin yace da kudaden suka shigo, sai da ya tafi banki don fada musu amma suka ce masa ya rike kudin
- Bayan watanni tara, bankin sun gano kuskure akayi kuma sun ce masa ya dawo da kudin
A ranar 29 ga Disamba, 2020, Russell Alexander, ya yi mamakin yadda aka fara tura masa kudi £110,000 (N60.7 million), cikin asusun bankinsa.
Ba tare da bata lokaci ba ya garzaya Bankin Barclays dake Ingila domin sanar da su abinda ya faru.
Timesnow News ta ruwaito cewa bankin ta fadawa Russell ya tafi ya rike kudin saboda kudin gado ne, ashe kuskure sukayi.
Kawai sai Mr Russell ya garzaya kasuwa ya sayi makeken gida a watan Yuni, 2021.
Banki tace ya dawo da kudin
Bayan watanni tara, Bankin Barclays ya gano cewa kuskure akayi kuma ya umurce Mr Russell ya dawo da kudin.
A cewar DailyMail, bankin yace lallai kuskure yayi wajen turawa Russell kudi kuma an sake tafka wani kuskuren wajen fada masa ya rike kudin.
Bankin sun samu nasarar kwashe kudaden dake asusunsa saboda ya ajiye daidai kudi tare wasu yan canji ciki.
Yanzu sun bashi kyautan £500 (N276k) ya rage zafi.
Mutumin yace basu kyauta masa ba
Mutumin wanda mazaunin Norfolk a Birtaniya ne yace bankin bai kyauta masa ba saboda sun bata masa tsarin rayuwa.
Yace:
"Na yi mamakin lokacin da kudin suka shigo, amma da na je banki har sau biyu nace su duba, sun ce in kashe kudin kawai."
Wani dan Najeriya, Julius Eze, ya mayar da kudi N2.5m da aka tura masa asusun bankinsa
A bangare guda, wani matashi dan Najeriya, Julius Eze, ya baiwa mutane mamaki bisa wani abin ban sha'awa da yayi.
Tsakanin ranar Juma'a, 9 ga Yuli da Asabar 10 ga Yuli, bayan an kulle bankuna, ya ga an tura masa kudi N2.5m cikin asusunsa.
Ba tare da bata lokaci ba ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ranar Litinin, 12 ga Yuli zai mayar da kudin banki.
Asali: Legit.ng