EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Sojoji da kisan kiyashi
- Binciken EndSARS da kwamitin da Gwamnatin Legas ta kafa ya yi, ya zargi jami’an tsaro da kisan gilla
- Rahoton kwamitin Doris Okuwobi ya tabbatar da cewa sojoji sun hallaka ‘yan zanga-zanga a kofar Lekki
- Sojoji sun buda wuta sun kashe mutane rututu, sannan suka boye gawawwakinsu domin ayi rufa-rufa
Lagos - Kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Legas ta ba alhakin binciken abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya kammala aikinsa.
VOA Hausa tace binciken kwamitin ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin wadanda suka yi zanga-zanga a kofar shiga Lekki.
Kwamitin da Alkali Doris Okuwobi ta jagoranta ya tabbatar da cewa sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zanga a bakin kofar shiga wannan unguwa a Legas.
Hakan ya sa tsautsayi ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da suka fito zanga-zangar lumana domin yin Allah-wadai da zaluncin jami’an ‘yan sanda a Najeriya.
Matasan sun zargi dakarun SARS da zalunci, suka ce su na tare mutanen da aka gani dauke da komfuta, ana jifarsu da zargin damfara, har a harbi wasunsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamiti ya gabatar da dogon rahoto
Wannan rahoto mai shafuka sama da 300 da kwamitin binciken ya gabatar, ya bayyana yadda jami’an tsaro suka aukawa masu zanga-zangar ta lumuna.
Rahoton yace jami’an tsaron da ake zargi da laifi sun hada da sojojin kasa da dakarun ‘yan sanda.
Ta'adin da jami'an tsaro suka yi a Lekki
Jami’an tsaro sun harbi Bayin Allah barkatai a wajen wannan zanga-zanga, bayan haka suka dauke gawawwakin da harsasan bindiga, domin birne sawunsu.
Kwamitin yace a ranar 20 ga watan Oktoban 2021, sojoji sun buda wuta ga mutanen da ba su rike da wani makami sai tutar Najeriya, suna rera taken kasarsu.
EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas
Wannan kwamiti na musamman ya zargi jami’an tsaro da hana bada motocin asibiti, a taimakawa masu rauni, a karshe ya ba gwamnati shawarwari.
Shawarar da MURIC ta ba masu zanga-zanga
A lokacin da aka ruguza dakarun SARS saboda zargin da ake yi mata, kungiyar nan MURIC ta yi magana ta na kiran a janye zanga-zangar #EndSARS da ake yi.
MURIC mai wayar da kan jama’a kan hakkokin musulmai, ta gargadi masu wannan zanga-zanga da cewa su yi hattara da mugun nufin wasu da suka shiga rigarsu.
Asali: Legit.ng