Kawai Don Yana Musulmi, FFK Ya Kare Sheikh Pantami Kan Matsayin Zama Farfesa
- Femi Fani Kayode ya nuna goyon bayansa kan matsayin da aka baiwa ministan sadarwa, Sheikh Pantami, na zama Farfesa
- Tsohon ministan yace kungiyar ASUU na kokarin saka banbancin addini, amma Pantami ya cancanci wannan matsayin
- ASUU dai ta nuna rashin amincewarta bisa naɗa Pantami a matsayin Farfesa da jami'ar FUTO dake Owerri ta yi
Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya nuna goyon bayansa ga matsayin Farfesa da aka baiwa ministan sadarwa, Sheikh Pantami.
FFK kamar yadda ya yi kaurin suna, ya yi kokarin kare Pantami daga matsin lambar da yake sha a wurin kungiyar malaman jami'o'i ASUU.
Wannan na kunshe ne a wani sako da FFK ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook ranar Talata.
Me FFK ya faɗa game da Pantami?
A rubutun da ya buga, Femi Kayode yace:
"Wai me ministan sadarwa Isa Ali Pantami ya yi wa kungiyar ASUU? Yaushe wannan kiyayyar zata zo ƙarshe? Ko dan saboda shi musulmi ne, ni nasan Pantami sosai kuma ya cancanci zama Farfesa."
"Ya kamata mu rinka kallon kowa da soyayya ba wai ƙiyayya ba. Karerayi, yada labarai marasa tushe balle makama, nuna banbancin addini ko kabila ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba a ƙasa."
Wane mataki ASUU ta ɗauka kan Pantami?
A baya kungiyar Malamam jami'o'i ASUU, reshen jami'ar FUTO dake Owerri ta tabbatar da cewa naɗa Pantami a matsayin Farfesa yana kan ƙa'ida.
Sai dai kungiyar ta ƙasa ta nesanta kanta da matakin baiwa ministan matsayin farfesa da jami'ar ta yi.
Amma kuma yan kwanakin nan, ASUU ta bayyana cewa sam Sheikh Pantami bai cancani zama Farfesa ba, domin bai bi ƙa'idoji da kowa ke bi ba kafin kaiwa matsayin.
ASUU ta kuma kafa kwamiti na musamman da zai yi bincike kan naɗin Pantami, da kuma yadda aka bi aka bashi wannan matsayi.
A wani labarin kuma Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023
Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023.
Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata.
Asali: Legit.ng