Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

  • Wani matashi, Wajeeh Mahmood ya faranta wa iyayen sa rai yayin da ya nuna musu sakamakon jarabawarsa ta makarantar zama kwararren lauya
  • Daga mahaifinsa har mahaifiyarsa sun nuna matukar farin cikin su bayan ganin nasarar da dan nasu ya samu
  • Lauyan mai karancin shekaru ya ce bai yi tunanin sakamakon jarabawar sa zai yi kyau kwarai kamar yadda ya gani ba, don a tsorace ya ke

Wani matashi, Wajeeh Mahmood, ya duba sakamakonsa na karshe a makarantar kwarewa a aikin lauya a gaban iyayensa.

Kafin ya bude sakamakon wanda yadu a wani bidiyo a LinkedIn, mahaifinsa da mahaifiyarsa sun rungume juna cike da fargaba.

Farin ciki mara misaltuwa yayin da wani matashi ya duba sakamakon jarabawarsa tare da iyayensa
Farin ciki mara misali yayin da wani matashi ya duba sakamakon jarabawarsa tare da iyayensa. Hoto: LinkedIn/WajeedMahmood
Asali: Facebook

Yanzu zan iya murabus

Yayin da Wajeeh ya nuna musu sakamakon jarabawar tasa wacce ya yi ta neman kwarewa a fannin lauya a California, sun daga shi sama yayin da mahaifiyarsa ta rungume shi.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahaifinsa ya ce yanzu zai iya yin murabus daga aikinsa tunda dan sa ya zama lauya cikakke.

Take a wurin, mahaifiyarsa ta daga waya ta fara sanar da ‘yan uwa da abokan arziki labarin mai dadi.

‘Yar uwarsa kuwa ta bayyana farincikinta har tana rike shi yayin da ta ga nasarar da ya samu. Ga bidiyon a nan.

Legit.ng ta tattaro tsokacin da mutane suka dinga karkashin wallafar kamar haka:

Joseph Adewoyin ya ce:

“Barka Mahmood! Wannan babban abin farin ciki ne (Yanzu haka hawaye ne a idanuna). Mungode da wannan wallafar."

Edmundo R. Garcia ta ce:

“Barka Wajeeh.”

Arouj F ya ce:

“Gaskiya iyaye sun fi kowa son ci gaban dan su."

Howard Miller ya ce:

“Barka, ina maka fatan alheti a sauran al’umuran rayuwarka.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164