Abubuwa 60 da suke jawo yawan mutuwar aure – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Shehin malamin addinin musulunci, Aminu Ibrahim Daurawa ya yi wani rubutu, inda ya kawo wasu daga cikin musababban mutuwar aure a Najeriya.
A wani rubutu da malamin ya yi a shafinsa mai taken 'abubuwa sittin (60) da suke kawo mutuwar aure', ya jero wasu dalilan yawan mace-mace a kasar nan.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi aiki a hukumar HISBAH ta jihar Kano, wanda wannan ya ba shi damar fahimtar dalilan sabani tsakanin masu aure.
Irin abin da ya gani ne ya sa har malamin ya bude cibiya domin gyara rayuwar ma’aurata. An sa cibiyar suna ‘Love & mercy school for marriage counseling.’
A rubutun na sa, Aminu Daurawa ya raba wadannan musababban mutuwar aure zuwa rukuni uku; na kafin aure, cikin aure da matsalolin bayan an yi aure.
Daga cikin dalilan da Aminu Ibrahim Daurawa ya kawo akwai auren dole, miyagun ala’adu, matsaloli daga surukai da kuma sauran ‘yanuwan ma’auratan.
Su menene ke jawo aure ya mutu?
1. Al’adu
2. Rashin Ilimin Zamantakewar Aure
3. Rashin Zabin Matar Kirki Ta Gari
4. Auren da babu Soyayya Daga Miji Ko Mata
5. Gaggawar Yin Aure Batare Da Mutum Ya Shirya Ba
6. Banbancin Ilimi
7. Rashin Binciken Halin Miji Kafin Aure
8. Rashin Binciken Halin Mata Kafin Aure
9. Matsalar Iyayen Miji
10. Matsalar Iyayen Mata
11. Matsalar Dangin Miji
12. Matsalar Dangin Mace
13. Rashin Tsafta
14. Rashin Iya Kwalliya
15. Rashin Iya Magana
16. Rashin Ciyarwa
17. Rashin Iya Kwanciyar Aure
18. Rashin Adalci
19. Goyon Kaka (Yar Shagwaba)
20. Auren Kisa Wuta
Sauran dalilan sun hada da larurar rashin lafiya, rashin bincike, wasa da hakkoki, kazanta, kishi, rashin tarbiya.
21. Zaman Gidan Haya
22. Ruwan Ido Wajen Neman Aure
23. Auren Bariki
24. Auren Mace Don Kudinta
25. Auren Dole
26. Matsalar Talauci
27. Matsalar Qawaye
28. Zafin Kishi
29. Rashin Haihuwa
30. Rashin Ladabi
31. Rashin Kunya
32. Shaye-Shayen Kayan Maye
33. Kannen Miji
34. Kannen Amarya
35. Abokan Miji
36. Sata
37. Gulma
38. Tsananin Damuwa
39. Rashi Lafiyar Mace Wajen Gamsar Da Miji
40. Rashin Lafiyar Miji Wajen Gamsar Da Matarshi
Idan aka samu wasu daga cikin wadannan matsaloli da suka hada da cin amana, rashin wadata, da zafin kishi da mugun zato, babu mamaki a ji igiyar aure ta katse.
41. Sharrin Bokaye
42. Rashin Shawara Tsakanin Miji Da Mata
43. Aikin Mace (Ta Zama Yar Kasuwa Ko Ma'aikaciya)
44. Rashin Ilimi Da Samun Wayewa Akan Aure
45. Rashin Daukar Nauyin Iyali Wajen Basu Haqqi
46. Cin Bashi Ayi Aure
47. Yawan Tafiye-Tafiye
48. Yawan Zuwa Unguwa
49. Cin Amanar Aure Daga Miji Ko Mata
50. Shigar Da Qawaye Ko Abokai Cikin Harkar Iyali
51. Rashin Kula Da Addini
52. Girman Kan daya Daga Cikin Ma'aurata
53. Rashin daukar Aure A Matsayin Ibada
54. Butulci Da Manta Alheri
55. Samun Larura Ko Wani Ciwo Mai Tsanani
56. Yawan Shigar Iyaye Cikin Harkar Aure
57. Al mubazzaranci
58. Rashin Godiya
59. Mummunan Zato
60. Rashin Nuna Tausayi Da Damuwa Da Juna.
A karshe, Daurawa ya roki Allah (SWT) da ya daidaita tsakanin ma'aurata, Ya bada zaman lafiyar aure.
A wani rubutu da Malam Abubakar Sani Abdullahi ya yi, ya kawo dalilan da suka sa hatsi suke kara tsada a Najeriya, ya hada da shawara ta musamman ga jama'a.
Masanin ya bayyana abin da ya ke jawo tsadar kayan abinci, baya ga kira da jan kunne ga manoma da magidanta a kan abin da ya kamata su yi a shekarar badi.
Asali: Legit.ng