Yadda ginin Ikoyi mai hawa 21 ya rushe, Leburan da ta rutsa da shi ya magantu
- Wani lebura wanda ginin Ikoyi mai bene hawa 21 ya rushe a gaban idon sa yayin da su ke aiki a cikin ginin ya bayyana yadda lamarin ya auku dalla-dalla
- A cewarsa an hana shi bayyana yadda lamarin ya auku amma su na tsaka da aiki a wani ginshikin ginin da ke kasa suka ji alamar rugujewa
- Ya ce shi da abokin aikin sun yi kokarin tserewa yayin da ginin yake rushewa amma abin ya ci tura don zamewa ya yi ya fadi, da taimakon mai gadi aka cece shi
Legas - Daya daga cikin wadanda su ka samu nasarar tsira yayin da ginin bene mai hawa 21 na Ikoyi ya rushe ya bayar da bayani akan yadda lamarin ya auku, bisa ruwayar Premium Times.
A cewar sa, ya na tsaka da aikin gyaran wani ginshikin ginin tare da abokin aikin sa a kasa su ka fara jin ginin ya na rushewa.
A hirar da Premium Times ta yi da shi ya ce an bukaci ya yi shiru akan lamarin don gudun abinda zai iya biyo baya.
Ya shaida cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Muna aiki da abokin aiki na lamarin ya faru, duk da ban taba tattaunawa da wani a kai ba. A ranar muna aiki da Injiniya Kola da Injiniya Ike bayan sun umarci mu rushe wani ginshikin ginin ya fara rugujewa lamarin ya auku.
“Sun bukaci mu rushe ginshikin don mu sake wani inda su ka ce babu abinda zai faru. Muna tsaka da aikin ne muka ji alamar rugujewa.
“Garin guduwa daga wurin na zame na fadi, da taimakon mai gadin wurin na rayu. Ya daura ni bisa babur din haya sannan ya kai ni asibiti.”
Yace mai ginin ya san batun lalacewar ginshikin
Ya bayyana yadda mai ginin, Femi Osibona ya san halin da ginin yake ciki. Kuma shi ya sa injiniyoyin su sa a rushe ginshikin da suke aiki a kai.
A cewarsa, mai ginin ya je wani taro ne a lokacin da lamarin ya auku.
Ya kara da bayyana yadda tsautsayi ya ritsa da masu bautar kasar (Sam da Shola) da ginin ya rushe da su.
Bayanin Leburan ya kara nuna asalin yadda lamarin ya faru. A kalla gawawwaki 44 ne aka samu a rusashen ginin yayin da mutane 15 su ka raunana a ranar 1 ga watan Nuwamba.
A makon da ya gabata, Gwamna Babajide Sanwo Olu ya shirya wata kwamitin mutane 6 don bincike mai zurfi akan asalin yadda lamarin ya auku.
Asali: Legit.ng