EFCC ta koma kotu da tsohon Minista, wasu 4 saboda cin kudin Diezani Madukwe a zaben 2015
- EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa tana shari’a da mutum biyar kotun tarayya a Yobe
- Hukumar tace wadannan mutane sun karbi N450m a hannun Diezani Alison-Madueke a lokacin zaben 2015
- Da aka shiga kotu, lauyan da ya tsayawa wadanda ake kara ya bukaci beli, an daga zama sai shekarar 2022
Yobe - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta sake gurfanar da tsohon Minista, Abdu Bulama a gaban Alkali.
A wani jawabi da mai magana da yawun bakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, yace an gurfanar da Abdu Bulama a kotun tarayya da ke Damaturu, Yobe.
Uwujaren yace hukumar ta EFCC ta hada da wasu mutane hudu; Abba Tata, Muhammad Mamu, Hassan Jaks da wani tsohon kwamishina, Mohammed Kadai.
Alhaji Abdu Bulama ya taba rike mukamin Ministan kimiyya da fasaha na tarayya, shi kuma Mohammed Kadai ya yi kwamishinan raye karkara a jihar Yobe.
Sun ci kudin zaben Jonathan - EFCC
Jaridar Premium Times tace EFCC tana zargin wadannan mutan da laifuffuka bakwai. Daga ciki shi ne sun karbi N450m a hannun Diezani Alison-Madueke.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton yace wadannan mutane sun karbi wadannan kudi ne domin su taimakawa shugaba Goodluck Jonathan lashe zaben shugaban kasa na 2015 a Yobe.
Alhaji Kadai shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Goodluck Jonathan a 2015, yayin da sauran mutane uku suna cikin ‘yan kwamitin na jihar Yobe.
Sai 2022 za a cigaba da shari’a a kotu
Hukumar EFCC tace laifuffukan da ake zargin wadannan mutane da aikatawa sun ci karo da sashe na 18 (a) na dokar safarar kudi da aka kawo a shekarar 2011.
Da aka gurfanar da wadannan mutane a kotu, sun fadawa Alkali cewa ba su aikata laifin komai ba. Alkali mai shari’a, A. Aminu ya daga karar sai Junairun 2022.
Lauyan EFCC, Mukhtar Ahmed ya bukaci a sa ranar shari’a, yayin da E. A. Adenitan yace ya na neman a bada belin wadanda ake tuhuman, kafin a daga shari’ar.
Kwamiti na bidar Abba Kyari
Dazu aka ji cewa ana neman DCP Abba Kyari a gaban kwamitin binciken EndSARS saboda wani mutumi da ake zargi da laifi ya bace a hannun ‘Yan Sanda a Abuja.
A 2018 yaran Abba Kyari suka kama Morris Ashwe, har yau ba a sake jin labarinsa ba. Wannan ya sa 'yanuwan wannan bawan Allah suka kai karar IRT wajen kwamiti.
Asali: Legit.ng