Kungiya tana so kotu ta hana Buhari kashe N26bn a kan abinci da zirga-zirga a 2022
- Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta sake karar gwamnatin Najeriya a kotu.
- Kungiyar tace shugaban kasa zai batar da N26bn a kan cefenen abinci da kudin man jiragen sama a 2022.
- SERAP na kukan wadannan kudi sun yi yawa, ta bukaci Alkali ya hana fadar shugaban kasa kashe su.
Abuja - Kungiyar SERAP da ta yi fice wajen kare hakkin al’umma a Najeriya ta shigar da kara a babban kotun tarayya na Abuja a kan kasafin kudin 2022.
Jaridar Vanguard tace SERAP na so a hana shugaban kasa Muhammadu Buhari kashe Naira biliyan 22 a shekara mai zuwa a cefanen abinci da zirga-zirga.
Naira biliyan 22 aka warewa fadar shugaban kasa domin alawus, sayen kayan abinci da na jin dadi da tafiye-tafiye a cikin Najeriya da kasashen ketare.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kungiyar ta shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1361/2021 a kotun. Har yanzu ba a sa ranar da za a fara yin shari’ar ba.
Hukumar dillacin labarai tace Kolawole Oluwadare da wata lauya Adelanke Aremo suka gabatar da wannan kara a gaban kotun tarayya a madadin SERAP.
Wannan kungiya ta koka kan yadda gwamnati take cigaba da cin bashin kudi domin a cike gibin da ke cikin kasafin kasar, bayan ta ki rage facakar da take yi.
Rokon da lauyoyin SERAP suke yi
“A matsawa shugaban kasa ya rage kasafin kudin N26bn da aka warewa fadar shugaban kasa domin tafiye-tafiye, cin abinci da kayan dadi.” – SERAP.
Idan an yi haka, kungiyar tana so gwamnatin tarayya ta aikawa majalisar tarayya sabon kundin kasafin kudi wanda yake kunshe da wannan ragin da aka yi.
Bugu da kari, lauyoyin SERAP suna so Alkali ya tursasawa Muhammadu Buhari ya fito da abin da asibitin fadar shugaban kasa ya ci tun daga 2015 har zuwa yau.
SERAP tana so a karkatar da wannan N26bn wajen gyara sauran asibitocin kasar. SERAP tace wannan kudi ya zarce abin da aka warewa asibitocin koyon aiki 14.
Nawa aka warewa manyan asibitocin koyon aiki?
UNILAG Teaching Hospital—N1.69bn; ABU Teaching Hospital—N2.38bn; University College Hospital, Ibadan—N1.49bn; sai UNN Teaching Hospital—N1.38bn.
UNIBEN Teaching Hospital—N1.35bn; OAU Teaching Hospital—N1.35bn; UNILORIN Teaching Hospital—N982m; UNIJOS Teaching Hospital—N908m.
Sai kuma University of Port Harcourt—N1.14bn; UNIMAID Teaching Hospital—N986m; da kuma asibitin Dan Fodio University Teaching Hospital—N987m.
Ragowar su ne Aminu Kano Teaching Hospital—N2.49bn; da UNIABUJA Teaching Hospital—N1.90bn; da asibitin nan na ATBU Teaching Hospital—N947m.
Asali: Legit.ng