Hameed Ali zai tarawa Gwamnatin Buhari harajin Naira Tiriliyan 2 a cikin shekara daya

Hameed Ali zai tarawa Gwamnatin Buhari harajin Naira Tiriliyan 2 a cikin shekara daya

  • Hukumar kwastam mai yaki da masu fasa-kauri tana sa ran samun Naira tiriliyan 2 a shekarar 2022
  • Jihohin Kudu maso yamma za su tattara mafi yawan wannan kudi, har sama da Naira tiriliyan 1.5.
  • Gwamnatin Najeriya ta na samun haraji daga iyakokin Apapa, PTML, Tin Can, Tin Can II da na Seme.

FCT, Abuja - Hukumar kwastam mai yaki da masu fasa-kauri tana shirin samun Naira tiriliyan biyu a matsayin kudin shigar gwamnati a shekara mai zuwa.

Wani rahoto da ya fito daga Punch ya bayyana cewa mafi yawan wannan kudi za su fito ne daga iyakokin da ake da su a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Kamar yadda jaridar ta bayyana a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, 2021, ana sa ran iyakokin Legas, Ogun, Ondo da kuma jihar Oyo za su kawo 80% na kudin.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Alkaluman da aka samu daga gidan kwastam sun nuna jihohin nan hudu ne ke da alhakin 80.48% na kudin shigan. Jihohin sun yi iyaka da teku da Benin.

Abin da rahoton 2022 ya kunsa

“Alkaluman sun nuna daga cikin Naira tiriliyan 2 da za a samu a shekarar, Naira tiriliyan 1.6 za su fito ne daga yankin Kudu maso yamma.”
Hameed Ali da Buhari
Hameed Ali da Shugaban kasa Hoto: www.informationng.com
Asali: UGC

“Naira biliyan 264.2 daga yankin kudu maso kudu, da Naira biliyan 36.53 daga kudu maso gabas.”
“NCS tana sa ran samun Naira biliyan 35.35 daga Arewa maso yamma, Naira biliyan 20.21, sai Naira miliyan 662 daga Arewa maso gabas.”

Jihohin Kudu maso yamma za su fito da 81%

Abin da hukumar za ta sau daga Legas kadai ya kai 75%, yayin da Ogun, Ondo, da jihar Oyo za su bada gudumuwar kusan 5% daga ofisoshi 14 da ke yankin.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi tafiya, Osinbajo ya jagoranci FEC, an amince a kashe N47bn a kan wasu ayyuka

Harajin da kwastam take samu ya kasu ne tsakanin iyakokin Apapa (30.359%), PTML (11.911%), Tin Can (25.367%), da kuma dayan iyakar Tin Can II (1.143%).

Sai iyakar Kirikiri (1.502%) da na Lagos Industrial (1.065%). Gwamnatin Najeriya tana samun kudi a tashar jirgin sama na Murtala Muhammad da iyakar Seme

Abin da ake samu a Arewa maso tsakiya da Arewa maso yamma bai kai 3% ba. Harajin da ke shigowa Najeriya ta iyakokin Arewa maso gabas bai kai 1% ba.

Ma'aikata suna kuka da Gwamnatin Kogi

A makon nan aka ji yadda wasu malamai da ma'aikata suke kuka da Gwamnatin Kogi, sun ce ana zaftare masu kaso mai tsoka daga cikin albashinsu a duk wata.

Ama kuma Gwamna Yahaya Bello yace babu wani ma’aikaci da yake bin shi bashin kudi. Gwamnan yace da ana bin shi bashi, da ana ta yin zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng