Buhari ya yi tafiya, Osinbajo ya jagoranci FEC, an amince a kashe N47bn a kan wasu ayyuka
- Majalisar FEC ta zauna kamar yadda ta saba kowane mako a ranar Laraba 3 ga watan Nuwamba, 2021.
- A wajen wannan taro, an amince gwamnatin tarayya za ta batar da Naira biliyan 47 a kan wasu kwangiloli.
- Muhammmadu Buhari ya yi tafiya, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron.
Abuja - A zaman da aka yi ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, 2021, majalisar FEC ta amince a kashe Naira biliyan 47 a kan wasu kwangilolin gwamnati.
This Day ta fitar da rahoto da ya bayyana cewa jami’ar Abuja da babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Jabi, Abuja suna cikin wadanda za su amfana.
Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya shaidawa manema labarai cewa an amince da takardun da ya gabatar, daga ciki akwai na sayen kayan aiki.
Sanata Hadi Sirika yace hukumar NAMA za ta kashe fam €14,428,218.17 kimanin N28,039,080,799.40 a kudin gida wajen kawo na’urorin zamani.
Sauran kwangilolin sun hada da na’urorin da za a sa a filayen tashin jirgin saman Murtala Mohammed da Nnamdi Azikiwe wanda za su ci Naira biliyan 5.8.
Za a saye motocin aikin kwastam
Premium Times tace Clement Agba ya shaidawa ‘yan jarida majalisar FEC ta amince a kashe N1, 554,200,000 wajen sayen wasu motoci 46 na gidan kwastam.
“A yau FEC ta yarda a sayo motoci 46 da jami’an kwastam za su yi aiki da su. Kamfanin Messrs. Elizade Nigeria aka ba kwangilar kan N1, 554,200,000.” – Agba.
Ana sa ran cewa wadannan motoci za su taimakawa hukumar kwastam wajen yin aiki da kyau. Hakan yana nufin gwamnatin Najeriya za ta samu karin kudin-shiga.
Bayan haka, Femi Adesina yace an amince a gina sabon ofishin manyan ma’aikata a jami’ar tarayya ta Abuja, da kuma katafaren dakin taro mai cin mutum 1000.
Kamfanin Messrs Hilkam Engineering Consultancy Ltd aka ba kwangilar a kan N2, 354,247,466.76.
Akwai ayyukan da za a yi na samar da wuta a asibitin Federal Medical Center, Jabi a kan N768,906,174.71 da gyaran titin Sokoto – Ilela da zai ci N8,450,829,974.9.
Buhari ba ya Najeriya
A farkon makon nan aka ji shugaba Muhammadu Buhari ya bar Najeriya, ya je birnin Glasgow, kasar Scotland domin halartan taron sauyin-yanayi da ake yi.
Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci wannan taro na jiya kamar yadda aka saba idan Muhammadu Buhari ba ya kasar.
Asali: Legit.ng