Babbar Magana: Matasa sama da 172 sun haukace a jihar Zamfara

Babbar Magana: Matasa sama da 172 sun haukace a jihar Zamfara

  • Hukumar NDLEA ta bayyana cewa aƙalla matasa 172 ne suka kamu da cutar tabin kwakwalwa a jihar Zamfara cikin shekaru 6
  • A cewar hukumar akwai wasu da yawa dake asibitoci neman lafiya duk saboda shan kwayoyi ba bisa ƙa'ida ba
  • Ta ce ya zama wajibi al'umma ta tashi tsaye wajen yaƙi da wannan halayya da kuma taimaka wa waɗan da suka faɗa cikin matsala

Zamfara - Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla matasa 172 suka samu taɓin kwakwalwa saboda shan kwayoyi ba kan ƙa'ida ba cikin shekara 6 a jihar Zamfara.

Mataimakin kwamandan yaƙi da shan miyagun kwayoyi na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen Zamfara, Ladan Hashim, shine ya bayyana haka ranar Alhamis.

Mista Ladan, yace hukumar NDLEA reshen jihar Zamfara ta kai matasa da dama asibitin mahaukata domin kula da su.

Kara karanta wannan

Hukumar NAFDAC zata fara kamen masu sana'ar tallan kwayoyi a kan hanya a jihar Kaduna

Hukumar NDLEA
Babbar Magana: Sama da matasa 170 ne suka haukace a jihar Zamfara Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ladan ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taro mai taken, 'Ɗalibai zasu kawo kyakkyawan canji a yaki da shan miyagun kwayoyi a makarantar kwalejin lafiya ta Zamfara.'

Wane nasarori NDLEA ta samu a Zamfara?

A cewarsa daga watan Janairu zuwa Satumba, 2021 hukumar ta kama mutane da dama, maza 211 da kuma mata 10 duk masu ta'amali da miyagun kwayoyi.

Ya kuma ƙara da cewa a shekarar 2020, hukumar ta samu waɗan da suka sami taɓun kwakwalwa 14, kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

Yace:

"Sabida haka masu shan kwayoyi ba bisa ƙa'ida suna bukatar taimakon mu, mu fahimtar da su, kuma mu taimaka musu su samu lafiya ta hanyar ba su kulawa ."
"Da yawan matasan mu suna gidan yari, wasu kuma suna asibitoci neman magani, wasu kuma da yawa sun kamu da manyan cututtuka kamar lalacewar kunhu ko ciwan zuciya da sauransu."

Kara karanta wannan

Jerin tituna 21 da za su ci makudan kudade, kuma gwamnatin Buhari ta amince a yi

"A wanna yanayin, hanya mafi sauki itace yin amfani da magunguna dai-dai da yadda masana suka yi umarni."

A wani labarin kuma Hukumar NAFDAC zata fara kamen masu sana'ar tallan kwayoyi a kan hanya a jihar Kaduna

NAFDAC tace irin waɗannan mutanen suna wasa da rayuwar al'umma, domin sun saɓa dokokin siyar da magani.

A cewar hukumar ya kamata mutane su gujewa siyan magani a kan hanya domin kula da rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262