Hukumar gidajen gyara hali ta saki hotuna da sunayen Fursunoni 122 da suka gudu daga Kurkuku

Hukumar gidajen gyara hali ta saki hotuna da sunayen Fursunoni 122 da suka gudu daga Kurkuku

  • An bayyana sunaye da hotunan wasu daga cikin Fursunonin da suka guda daga gidan yarin dake jihar Oyo
  • A karshen makon da ya gabata, yan bindiga sun balla gidan yari kuma sun saki dukkan wadanda ke ciki
  • Ministan harkokin cikin gida yayi alkawarin cewa sai an kamo dukkan wadanda suka gudu

Ibadan - Hukumar gidajen gyara hali ta saki sunaye da hotunan mutum 122 cikin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Abolongo dake jihar Oyo.

Punch ta ruwaito cewa hukumar ta saki hotunan ne a ranar Laraba, 27 ga Oktoba, 2021.

Amma hotunan da aka saki ba shine hotunan dukkan wadanda suka gudu ba.

Hukumar gidajen gyara hali ta saki hotuna da sunayen Fursunoni 122 da suka gudu daga Kurkuku
Hukumar gidajen gyara hali ta saki hotuna da sunayen Fursunoni 122 da suka gudu daga Kurkuku Hoto: Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 4 da balle gidan, 'Yan sanda sun cire bam a gidan gyaran halin Oyo

Hukumar Gidajen Yari ta bayyana adadin Fursunonin da suka gudu da wadanda aka damko

Hukumar gidajen gyara hali ta jihar Oyo, ta bayyana cewa Fursunoni 837 ne suka arce daga gidan yarin Abolongo sakamakon harin da yan bindiga suka kai daren Juma'a.

Kakakin hukumar, Olanrewaju Anjorin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, a Ibadan, rahoton NAN.

Olanrewaju yace dukkan Fursunonin dake sauraron gurfana gaban kotu 837 ne suka arce amma wadanda tuni aka yanke musu hukunci na nan ba'a shiga inda aka ajiyesu ba.

Yace kawo yanzu an damko mutum 262 cikin wadanda suka gudu, yayinda ake neman 575.

Adadin mutum nawa gidan yarin ke dauka?

Ya kara da cewa an gina gidan yarin ne a 2007 kuma asali mutum 160 zai dauka, amma yanzu mutane 907 ke zama.

"Daga cikinsu, mutum 837 na sauraran gurfana a kotu, mutum 64 kadai aka yankewa hukunci," Anjorin yace.

Kara karanta wannan

Mun damke manyan mutane da muke zargi da hannu a fasa gidan gyaran hali a jihar Oyo, Gwamna

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng