Sanusi ya saki maganganu, yace haramun ne a rika cire kudin tallafin fetur daga asusun hadaka

Sanusi ya saki maganganu, yace haramun ne a rika cire kudin tallafin fetur daga asusun hadaka

  • Tsohon sarkin Kano ya soki biyan tallafin man fetur da ake yi a Najeriya
  • Muhammad Sanusi II yace gwamnatin tarayya na saba doka da yin hakan
  • Sanusi II yana zargin cewa akwai badakala a tsarin na tallafin man fetur

Abuja - Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yace gwamnatin tarayya tana saba doka ta hanyar cire kudin tallafin fetur daga asusun hadaka na kasa.

Muhammad Sanusi II ya bayyana wannan a lokacin da ya tofa albarkacin bakinsa a matsayin jigon tafiyar SDG a taron tattalin arziki da aka shirya a garin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Malam Sanusi II yana sukar tsarin biyan tallafin man fetur a Najeriya.

Tsohon gwamnan babban bankin kasa na CBN yake cewa akwai rashin gaskiya da ake tafkawa a tsarin da gwamnati mai-ci ta dauka na biyan tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Wike ya yi kaca-kaca da mulkin Buhari, yace abubuwa ba su taba tabarbarewa haka ba

Abin da Khalifa Muhammadu Sanusi II ya fada

“Kudin nan da ake samu daga fetur suna shiga asusun hadaka ne, kuma gwamnatin tarayya ba ta da ikon da za ta biya tallafin mai a madadin tarayya.” – Sanusi II.
“Saboda haka maganar tsarin mulki ne domin wannan kudi ne da ya dace su tafi jihohi da kananan hukumomi. Akwai bukatar mu tsaida wadannan abubuwa”
“Na fadi wannan a lokacin da na ke gwamnan CBN a lokacin gwamnatocin baya. Abin da nake fada bai shafi gwamnatin da ta ke ci ba. A duba tallafin man fetur.”
Tsohon Sarkin Kano
Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: www.theafricareport.com
Asali: UGC

Me ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi?

A cewar tsohon mai martaban, biyan tallafin fetur yana da fuskar tattalin ariki da harkar shari’a.

Sanusi II ya yi kira a kawo karshen tsarin tallafin fetur da na lantarki, yace ya kamata kudin da ake batarwa su tafi ne cikin kasafin ilmi da na kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Mai zai iya kara tsada, Gwamnati za ta daina biyan tallafin fetur a tsakiyar shekara mai zuwa

Khalifan na Tijjaniya yace da Ibe Kachukwu yake Minista a 2015 ya taba cewa ana shigo da lita miliyan 30 na fetur, amma yanzu abin har ya kai lita miliyan 59.

Orji Uzor Kalu zai sake gwabzawa da EFCC

Dazu aka ji cewa tsohon Gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu zai fuskanci sabuwar shari’a a kan zargin wawurar Naira Biliyan 7.1 da Hukumar EFCC ta ke zarginsa.

Kotu ta taba daure Kalu na tsawon shekaru 12 a gidan maza, bayan wani lokaci sai ya fito. EFCC tana so a maimaita wannan shari'a domin a sake daure shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng