Bayan shekara 1, Rundunar soji ta ki mayar da Kanal din da ya halaka 'yan Boko Haram 377 bakin aikinsa
- Rundunar sojin Najeriya ta ki mayar da Kanal Auwal Suleiman bakin aikinsa bayan nasarar da yayi a kotun masana'antu da shekara 1
- Kamar yadda aka gano, hafsan sojan ya shirya kamen 'yan Boko Haram 377 a arewa maso gabas kafin a yi masa ritayar dole
- Rundunar ta dogara da Suleiman wurin samo bayanan sirri kuma shi ya kafa rundunar hadin guiwa ta JTF da ke Borno
Borno - Har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta mayar da Kanal Auwal Suleiman bakin aikin sa ba, shekara daya bayan kotun masana'antu a ke Abuja ta bayar da umarnin cewa a mayar da shi bakin aikinsa.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Suleiman ya na daga cikin sojoji 38 da aka tirsasa yi musu ritaya a watan Yunin 2016.
Bayan kai karar gaban kotu, Suleiman ya yi nasara a watan Fabrairun 2020 inda aka umarci rundunar sojin da ta mayar da shi matsayinsa na 2016.
Yayin yanke hukunci, Mai shari'a Sanusi Kado na kotun masana'antu da ke Abuja ya yi watsi da ikirarin cewa an yi wa hafsan sojan ritaya ne saboda ya wuce zama a rundunar da shekaru 18 inda yace babu shaida kan hakan.
PRNigeria ta tattaro cewa kafin a yi masa murabus, Suleiman ne ya kirkiro fitacciyar kungiyar jami'an tsaron hadin guiwa, JTF kuma ya shirya damke 'yan Boko Haram 377 a 2009.
Hakazalika, jami'in sirri ne da ya jagoranci ayyuka masu yawa wadanda aka samu nasara wurin yakar Boko Haram da kamen kwamandojinsu.
Rundunar sojin da bangaren binciken sirri sau babu adadi sun dogara da zakakurancin Suleiman tare da kwarewarsa wurin yakar ta'addanci.
Wani jami'in binciken sirri na rundunar ya sanar da PRNigeria cewa an soke zaben Suleiman matsayin mataimakin shugaban ayyukan majalisar dinkin duniya a Darfur a 2011.
An sake soke zaben Suleiman a matsayin mataimakin mai bada shawara kan harkokin tsaro a ofishin jakadancin Najeriya a Washington a 2012 saboda zaman shi jigon aikin yaki da ta'addanci a arewa maso gabas.
Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11
A wani labari na daban, jiragen yakin dakarun sojin sama na Najeriya, NAF, sun ragargaji wasu mayakan ta'addanci na ISWAP a yankin arewa maso gabas.
PRNigeria ta tattaro cewa jiragen saman sun saki ruwan wutar ne a tsibirin Tumbun, kusa da tafkin Chadi.
Wata majiyar rundunar sojin, ta ce bayan bayanai kwarara na sirri kan cewa mayakan ISWAP suna tattaruwa domin wani gagarumin taro a tsibirin Tumbun.
Asali: Legit.ng