Gwamnatin Buhari na tunanin yin afuwa ga mutanen da Janar Abacha ya bindige a 1995
Muhammadu Buhari ya dauko maganar yafe wa su Ken Saro Wiwa laifuffukansu
Shugaban kasar ya fadi wannan da ya zauna da dattawan kasar Ogoni a Aso Rock
Janar Sani Abacha ya kashe Saro-Wiwa da wasu mutum a 1995 da yake kan mulki
Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna yiwuwar yin afuwa ga Ken Saro-Wiwa da sauran ‘yan gwagwarmayar Ogoni da aka hukunta.
Shugaban Najeriya na duba yiwuwar yafe wa Ken Saro-Wiwa bayan sun mutu a shekarar 1995.
Jaridar Premium Times tace Muhammadu Buhari ya nuna hakan a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, 2021, da ya gana da wasu dattawan Ogoni a Abuja.
Mai martaba Godwin N.K. Giniwa wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan kasar Ogoni ne ya jagoranci wadannan manya zuwa fadar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Duk da mummunan abin da ya wakana, gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar yin afuwa domin a birne batun Ogono.” – Muhammadu Buhari.
“Baya ga haka, muna da niyyar yin afuwa da jawo al’umma a yunkurin gwamnatin nan na kafa tubulin yin sulhun gaskiya, a rufe maganar nan.”
“Wannan abin takaici ya auku a farkon shekarun 1990s, ya yi sanadiyyar da aka rasa mutanen Ogoni da-dama, abin da ya faru yana a ranmu.”
Kiran da Buhari ya ke yi
Buhari ya yi kira ga shugabannin da ke Neja-Delta su yi kokari wajen kare bututun mai da aka shimfida, yace yin hakan zai jawo wa mutanen wurin asara.
Vanguard ta rahoto shugaban kasar yana cewa gwamnatinsa za ta dage wajen ganin mutanen Ogoni sun cigaba da noma domin su samu na yin cefane.
A cewar Buhari, an ba kamfanin NPDC lasisin aiki da rijiyar man OML 11 domin bunkasa tattalin yankin.
Saro-Wiwa na cikin mutanen da gwamnatin Sani Abacha ta kashe, bayan an yi wani bincike da ya nuna suna da hannu wajen tada fitina a Nuwamban 1995.
Ken Nnamani ya rubuta littafi
A wani littafi da tsohon shugaban majalisa, Ken Nnamani ya rubuta, babban Jigon na APC ya bada labarin dakile tazarcen Shugaba Olusegun Obasanjo da ya yi.
Wasu suna ganin cewa shugaba Obasanjo bai yi niyyar mika mulki bayan ya yi shekaru takwas ba. Nnamani ya kaddamar da littafin na sa jiya a garin Abuja.
Asali: Legit.ng