Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11

Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11

  • Jiragen yakin sojin Najeriya 3 sun halaka 'yan ta'adda masu yawa a tsibirin Tumbun a tafkin Chadi
  • 'Yan ta'addan ISWAP din sun tattaru a jiragen ruwa 11 suna hanyarsu ta zuwa wani muhimmin taro
  • Rundunar Operation Hadin Kai sun samu bayanan sirri inda suka garzaya tare da jiragen yakinsu

Tumbun, Borno - Jiragen yakin dakarun sojin sama na Najeriya, NAF, sun ragargaji wasu mayakan ta'addanci na ISWAP a yankin arewa maso gabas.

PRNigeria ta tattaro cewa jiragen saman sun saki ruwan wutar ne a tsibirin Tumbun, kusa da tafkin Chadi.

Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11
Jiragen NAF sun yi wa 'yan ISWAP luguden wuta yayin da suke cikin jiragen ruwa 11. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wata majiyar rundunar sojin, ta ce bayan bayanai kwarara na sirri kan cewa mayakan ISWAP suna tattaruwa domin wani gagarumin taro a tsibirin Tumbun.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan ta'addan ISWAP da Ansaru ne suka sanya bam a layin dogon Abuja-Kaduna

Hakan yasa jiragen yaki karkashin Operation Hadin Kai suka shirya tsaf tare da sakar musu ruwan wuta, Daily Nigerian ta wallafa.

"Jiragen yakin sun yi nasarar sheke wasu yayin da wadanda basu mutu ba suka dinga neman dauki cike da tashin hankali," yace.

Bincike: 'Yan ta'addan ISWAP da Ansaru ne suka sanya bam a layin dogon Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, 'yan ta'addan kungiyar ta'addancci ta ISWAP tare da Ansaru ne suke da alhakin lalata layin dogon Abuja zuwa Kaduna, majiyoyi masu karfi na tsaro suka tabbatar wa da Daily Trust a ranar Alhamis.

Karaikainar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta gurgunta na wucin-gadi daga daren Laraba zuwa Alhamis bayan an gano cewa 'yan ta'adda sun sanya bam tare da tashin wani sashi na layin dogon.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu

Miyagun sun koma da sa'o'in farko na ranar Alhamis inda suka sake lalata wani sashi na layin dogon, lamarin da yasa hukumar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyukan ta.

Duk da NRC ta kwatanta lamarin da barnar mabarnata masu son lalata kayayyakin hukumar, majiyar tsaro mai karfi ta ce da hannun 'yan ta'adda a lamarin.

Wani babban jami'in tsaro ya tabbatar wa da Daily Trust cewa, a cikin kwanakin da suka gabata, jami'an tsaro sun tare da halaka wasu 'yan ta'addan da suka yi yunkurin saka bam a gadoji da layikan dogo a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: