Gowon, Obasanjo, Babangida, da Jonathan za su ci Biliyan 2 a kasafin kudin shekarar 2022
- Gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 2 a kan tsofaffin shugabannin kasa
- Janar Gowon, Ibrahim Babangida, Obasanjo da Jonathan za su amfana da kudin
- Muhammadu Buhari ya yi kasafin N16.4tr na shekarar 2021 – mafi yawa a tarihi
Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 2.3 a cikin kasafin kudin 2022 domin a ba tsofaffin shugabannin kasar da aka yi a Najeriya hakkokinsu.
Jaridar Reuben Abati tace tsofaffin shugabannin farar hula da soja da suke raye za su amfana da kudin.
Wadanda za su amfana da kudin sun hada da; Janar Yakubu Gowon, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdulsalami Abubakar.
Sai Ernest Shonekan da Olusegun Obasanjo da Dr. Goodluck Jonathan wanda ya bar mulki a 2015.
Yakubu Gowon, Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar sun yi mulki ne a zamanin soja. Sauran sun yi mulki a zamanin farar hula.
Cif Olusegun Obasanjo yana cikin shugabannin da suka samu damar yin mulki a gwamnatin soja da na farar hula. Na biyun shi ne Muhammadu Buhari.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, za a ayi amfani da wannnan kudi Naira biliyan 2.3 wajen biyan tsofaffin shugabannin kasar alawus dinsu na shekara.
Tsofaffin ma'aikata za su karbi hakkokinsu
Akwai kason Naira biliyan 4.502 da aka ware domin a biya tsofaffin shugabannin ma’aikatan gwamnati da sakatarori na din-din-din fanshonsu a 2022.
Haka zalika akwai Naira biliyan daya da za su tafi wajen biyan hakkokin tsofaffin gwamnatin tarayya.
A cikin wannan kaso, Naira biliyan 65 zai tafi shiga tsarin lamuni na Neja-Delta. Sannan za a kashe N350bn wajen daukar nauyin sojojin kasa da ‘yan sanda.
APC ta fara shiryawa 2023
An fara lissafin zabe mai zuwa na 2023 inda aka ji cewa babban jigon APC, Bola Ahmed Tinubu zai zauna da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Jam’iyyar APC za ta yi kokarin ganin ba a samu rikici wajen tsaida ‘dan takara a 2023 ba. Bisa dukkan alamu Bola Tinubu zai nemi takarar shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng