Labarai
Gwamnatin Bauchi ta sanar da lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a karshe watan Nuwamba. Bala Muhammad ya ce zai biya hakkokin ma'aikata a jihar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ba da takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa da mataimakinsa.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kashe mutum guda yayin da faɗa ya kaure tsakanin wasu jami'anta da ke bakin aiki da wani sojan Najeriya a jihar Ebonyi.
Babban Sufetan yan sanda, Kayode Egbetokun ya shigar da korafi kotu kan Sanata Andy Ubah da wata Hajiya Fatima kan zargin damfarar wani mai suna George Uboh.
Majalisar dokokin ta yi karatu na biyu ga kudirin dokar da zai sauya harkar zabe a Najeriya. Yan Najeriya mazauna ketare za su rika yin zaɓe saboda samuwar kudirin.
Majalisar dattijai ta yi amfani da sashe na 157 (1) na kundin tsarin mulkin kasar domin korar Yakubu Danladi Umar a matsayin shugaban kotun da’ar ma’aikata ta CCT.
Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar ilmi ta sanar da korar shugaban jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) da ke jihar Abia. Ta ce nadin da aka yi masa ya saba doka.
Wata malama mai koyar da ilimin addinin musulunci a wani kauye da ke Kano, Khadija Muhammad ta samu yabo daga jama'a kan sadaukar da kanta tare da ba ta tallafi.
Ministar harkokin mata, Imaan Suleiman-Ibrahim ta ce gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 112 domin tallafawa shirin samar da tsaro a makarantu.
Labarai
Samu kari