FUCAP: Unilever Ya Gada Gwiwa da UNICEF, An Tallafawa Matasa 900,000 a Najeriya
Shirin Future-X Unilever Campus Ambassadors (FUCAP) na kamfanin Unilever Nigeria Plc, tare da haɗin gwiwar UNICEF, ya tallafa wa matasa sama da 900,000 a Najeriya.
A karkashin shirin FUCAP, dubunnan daruruwan matasan sun samu hoto a kan dabarun samun aiki, fasahar zamani da ilimin kasuwanci da ake buƙata a duniyar aiki ta yau.

Source: UGC
Shirin FUCAP na Unilever da UNICEF
Wannan shiri, wanda ya shafe kusan shekaru biyu da rabi ana aiwatar da shi, ya dogara ne kan tsarin haɗin gwiwa mai ƙarfi da ya haɗa da YOMA na UNICEF, kafofin sada zumunta na Unilever da kuma cibiyoyin ilimi na jami’o’i da manyan makarantu.
Unilever na daga cikin manyan abokan hulɗar ƙasa da ƙasa na shirin Generation Unlimited (GenU), wata babbar ƙungiya ta haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ke taimaka wa matasa wajen samun ilimi, horo da aiki.
A Najeriya, shirin ya samu cikakken goyon bayan shugabanci a matakin ƙasa, inda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ke jagorantar kwamitin GenU Nigeria, abin da ke nuna ƙudirin gwamnati wajen bunƙasa rayuwar matasa.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Wasu manyan alkalai a Najeriya na iya shiga matsala da NJC ta fara bincikensu
Tasirin shirin FUCAP a jami'o'in Najeriya
Da yake jawabi a wani taron manema labarai, shugaban Unilever Nigeria, Tobi Adeniyi, ya bayyana shirin FUCAP a matsayin ingantaccen tsarin haɗin gwiwa da ya haɗa jagorancin gwamnati, ƙwarewar UNICEF a fannin ci gaban jama’a da kuma manufar Unilever ta inganta rayuwar al’umma.
A cewarsa, haɗa koyon ilimin zamani da hulɗar kai tsaye a harabar jami’o’i ya taimaka wajen faɗaɗa tasirin shirin.
Sama da ɗalibai 85,000 ne suka amfana da tarurrukan horarwa 30 da aka gudanar a jami’o’i da manyan makarantu, inda jakadun Future Career Ambassadors (FUCAs) na Unilever tare da cibiyoyin haɗin gwiwa suka jagoranta.
Adeniyi ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da manufofin dorewar Unilever na inganta rayuwa da samar da hanyoyin samun arziki, wanda ke taimakawa wajen cimma burin ci gaba mai dorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDGs), ta hanyar ba matasa damar samun ilimi da ƙwarewar da za su taimaka musu bunƙasa rayuwarsu.
Ya ce matasa su ne ginshiƙin makomar tattalin arzikin Najeriya, don haka Unilever na zuba jari a bangarorin da ke faɗaɗa damar koyon dabaru da shiga duniyar aiki cikin kwarin gwiwa.
UNICEF ta jaddada muhimmancin FUCAP

Source: UGC
Ita ma shugabar ofishin UNICEF ta Legas kuma jagorar GUN, Celine Lafoucriere, ta ce haɗin gwiwar UNICEF da Unilever na ci gaba da ƙarfafa matasa ta hanyar shirin FUCAP.
Ta bayyana cewa cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, an mayar da hankali wajen horar da matasa dabarun kasuwanci, fasahar dijital da shawarwarin sana’a.
A halin yanzu, FUCAP na aiki a jami’o’i 20 a faɗin ƙasar, inda yake cike gibin da ke tsakanin ilimin aji da buƙatun masana’antu, ta hanyar kawo ilimi na zahiri kai tsaye ga ɗalibai da samar musu da hanyoyin shiga aikin yi.
Ta ce ta wannan hanyar, ana gina tsari mai ɗorewa da ke ba matasa damar sauya wa daga matakin karatu zuwa samun kuɗin shiga cikin kwanciyar hankali.
Masu lura da harkokin ci gaban matasa na ganin cewa FUCAP ya zama misali na yadda haɗin gwiwar gwamnati, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kamfanoni masu zaman kansu za su iya haɗa ƙarfi domin magance matsalar rashin aikin yi da rashin ƙwarewa a tsakanin matasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng
