Ban San Aikin Mahaifina Ba: Faifan Bidiyon Wani Hamshikin Uba Ya Karade Kafar Sada Zumunta
- Bidiyon da ya karade kafar sada zumunta ta zamani ya jawo kace-nace a bayan da wani yaro ya wallafa bidiyon mahaifinsa
- A cikin faifan bidiyon, an gano wasu jerin motoci masu alfarma na mahaifin nasa, da sauran kayan kawa na zamani
- Yaron ya bayyana cewa bai san takamaimai aikin da mahaifin nasa yake ba, sai dai kullum yaga ya ce zai je wurin aiki
Wani dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ya daura faifan bidiyon mahaifinsa cikin yanayin alfarma.
Yaron mai suna Daniel East Coast ya daura faifan bidiyon mahaifinsa cikin shigan alfarma da wata dankareriyar mota mai tsada lokacin yake shirin fita zuwa aiki.
Sai dai a cikin bidiyon ya tabbatar da cewa shifa har yanzu ma bai san takamaiman aikin mahaifin nasa ba, kawai abunda ya sani kullum mahaifin nasa na shiga na alfarma da kuma tuka motoci masu dan karen tsada.
Bugu da kari, a cikin faifan bidiyon anga wani bangare na jerin motoci masu tsadan gaske a cikin gidan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rubuta cewa:
"Ace mutum yana tare da mahaifinsa amma baisan aikinsa ba, kawai sai dai kullum yasa kaya masu kyau ya fita wurin aiki"?.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu lokacin da suka ga wannan faifan bidiyon
@shelovesmichaelalot ya ce:
''Kai dai kawai kasan ana biya maka dukkan bukatunka".
@agiftfromvirgo_ ya rubuta:
''Duk wani dan Najeriya nasan yana da mahaifi hamshakin mai kudi''.
@theeforeign cewa ya yi:
'Mafi yawan mutane idan nace musu bansan rayuwar iyayen na nahiyar Afrika basa yarda''.
@neptunemami ya ce:
''Rayuwata ba zata barni na shakata yanda nake so ba, amma shi kuma yana shakatawa da dukiyarsa".
Likita Ya Yi Gargadi Kan Amfani Da Tukwanan Zamani na ‘Non-stick’, Bidiyon Ya Yadu
A wani labarin, Likitan Najeriya, Chinonso Egemba ya gargadi mutane a kan amfani da tukwanan 'non-stick' da cikinsu suka babbare.
A cewarsa, amfani da irin wadannan tukwane yana da matukar hatsari ga rayuwar mutane.
A cewar likitan, tukwanan an lullube su ne da sinadaran Polyfluoroalkyl substances (PFAS), wadanda bai kamata ace sun bare ba.
Da zaran an samu akasi sun fara barewa, hakan na nufin ba mai kyau bane, kuma sinadaran PFAS na iya haifar da cututtuka.
Asali: Legit.ng