N30,000 Kacal Muka Kashe: Sabbin Ma'aurata Sun Bayyana Auren Tattalin Da Sukayi

N30,000 Kacal Muka Kashe: Sabbin Ma'aurata Sun Bayyana Auren Tattalin Da Sukayi

  • Daurin aure wani sha'ani da mutane ke alfahari da shi matuka a rayuwarsu ta duniya
  • Dalilin haka yasa wasu ke kashe makudan Nairori wajen shirin aure da ciyar da bakin da suka gayyata
  • Amma shin daurin aure na bukatar kashe irin kudaden da ake kashewa a addini da al'ada?

Wasu sabbin ma'aurata sun bayyana irin tattalin da suka yi wanda cikin mintuna goma kacal suka kwashe ba tare da batawa jama'a lokaci ba.

Amaryar mai suna, Okpe Faith, ta bayyana cewa Naira dubu talatin (N30,000) suka kashe

Faith ta bayyana hakan a shafinta na Facebook ranar Juma'a inda ta baiwa masu niyyar aure shawara kada su hana kansu aure saboda rashin kudi.

A cewarta:

"Ga aurena na farko. A kotu muka yi kuma ko N30,000 bamu kashe ba, mutum biyu kacal suka yi shaida kuma gaba daya ko minti 10 ba'a yi ba aka kammala komai."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

"Idan abinda mutum zai iya kenan kawai yayi. Idan kai kirista ne, Fastonku zai iya muku addu'a kuma shikenan aure ya dauru, zaku iya fara rayuwarku."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Okpee
Sabbin Ma'aurata Sun Bayyana Auren Tattalin Da Sukayi Hoto: Okpe Faith
Asali: Facebook

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu:

Timothy Adu-ojo Akubo yace:

"Dukkan kyawun da kike shi. Babu alfahari, Allah ya albarkaceta da mutum mai kyawun hali, gaskiya kin yi aure mafi dadi a duniya."
Yar Uwata Uangiji ya albarkaci aurenta."

Bliss Anthony yace:

"Auren gargajiyane da kuka yi da. Nawa kuka kashe? Ku fada min lissafin kudin da kuka kashe. Ba wai auren kotun ba kadai. A fada mana wannan sai mu san ta ind amuka fara.."

Sanni FiBee Love yace:

"Amma ai kun yi auren turawa da na gargajiya ai? Nawa kuka kashe gaba daya. Ai tuni mun sani auren kotu basu da tsada."

Oluchi Onuoha yace:

Kara karanta wannan

Ban Son A Kashe Ni: Dan Chinan Da Ake Tuhuma Da Kisan Ummita Ya Bayyanawa Kotu

"Nima na tuna da haka. Na yi auren kotu da Dala 30 kadai kuma shaidu biyu kadai."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida