Wani Tsohon Bidiyon Biloniya Femi Otedola Cikin Motar Haya Ba Tare Da Fasinjoji Sun Gane Shi Ba Bayyana

Wani Tsohon Bidiyon Biloniya Femi Otedola Cikin Motar Haya Ba Tare Da Fasinjoji Sun Gane Shi Ba Bayyana

  • Mutane sun rika tattaunawa kan attajirin dan kasuwa Femi Otedola a kafafen sada zumunta a yau bayan wani tsohon bidiyonsa ya sake bayyana
  • Bisa dukkan alamu, attajirin dan kasuwan ya shiga motar haya da ke kira 'molue' a Legas amma babu wanda ya gane shi cikin fasinjojin
  • Wasu mutane da dama cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon sun ce babu yadda zai iya sake yin hakan a yanzu ba tare da an gane shi ba saboda ya kara yin suna

Wani tsohon bidiyon attajirin dan kasuwa Femi Otedola ya sake bulla a shafukan intanet, abin da ya farantawa mutane da dama rai.

Bisa dukkan alamu, wasu shekaru da suka gabata, fittacen dan kasuwan ya shiga motar haya 'molue' ba tare da fasinjojin da ke motar sun gane ko shi wanene ba.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Da Barayin Gwamnati Ke Boye Kudadensu a Najeriya

Wani Tsohon Bidiyon Biloniya Femi Otedola Cikin Motar Haya Ba Tare Da Fasinjoji Sun Gane Shi Ba Bayyana
Wani Tsohon Bidiyon Biloniya Femi Otedola Cikin Motar Haya Ba Tare Da Fasinjoji Sun Gane Shi Ba Bayyana a Intanet. Hoto: @FemiOtedola
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya nuna Otedola yana zaune kusa da wata mata wacce ke tallar kayayakinta ga mutanen da ke cikin motar hayan.

Otedola yana sanye da tufafi ne na yau da kullum hakan yasa ya saje cikin mutanen da ke motar cikin sauki.

Bayan ya isa inda zai sauka, dan kasuwar ya sauka daga motar hayan ba tare da kowa ya gane shi ba.

Kalli bidiyon a kasa kamar yadda Goldmynetv.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: