Kyakkyawan karshe: Yadda Mutuwa ta Dauki Matashin Limami a Tsakiyar Sallar Dare

Kyakkyawan karshe: Yadda Mutuwa ta Dauki Matashin Limami a Tsakiyar Sallar Dare

  • Wani Bawan Allah mai suna Sani Lawal ya yi sallama da Duniya a lokacin da yake yin sallar dare
  • Malam Sani Lawal ya rasu ne yayin da yake limancin sallar daren a wani masallaci da ke garin Zaria
  • Musulmai su na ta yi wa wannan Alaranman kyakkyawan zato bayan ganin irin karshen da ya yi

Kaduna - Legit.ng Hausa ta samu labarin rasuwar wani Alaranma mai suna Sani Lawal wanda ya rasu a lokacin da yake ibadar sallar dare a watan Ramadan.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga majiyoyi da dama, Sani Lawal ya rasu ne a daidai lokacin sujada, yana limancin sallar tahajjud a ranar Asabar dinnan.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin dazu da safe da kimanin karfe 8:00 na safe a unguwarsu da ke Layin MB, Samaru, karamar hukumar Sabon Gari, Kaduna.

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Kuma Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki Ya Rasa 'Ya'Yansa Biyu a Hatsari

Wani Aminin Marigayin yace ya bar masallacin bayan an yi raka'a takwas. sai kurum aka kira shi a waya, aka fada masa ai Liman ya fadi a yayin sujuda.

Legit.ng Hausa tuntubi wani abokin marigyain, wanda ya shaida mana wannan labari mara dadi.

Malam Anas Mansur ya san Marigayin, kuma ya tabbatar mana da cewa ya rasu ne bayan ya yi sujudar tilawar Al-kur’ani da ke cikin surar nan ta Al-Nahli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin Allah ne

A cewar Anas Mansur, kamar yadda ya yi bayani a Facebook, Marigayin mutumin kirki ne wanda al'ummar unguwar Samaru suke matukar bukatar ire-irensa.

Alaranma Sani Lawan
Alaranma Sani Lawan Hoto: Anas Mansur and theistanbulinsider.com
Asali: UGC

Sani Lawan ya samu shaidar cewa yana cikin matasan da ke yi wa yara masu tasowa tarbiya.

“Allah ya azurta shi da kyakkyawan karshen kamar yadda Allah SWT Ya ce duk wanda suke sallah a wani bangaren dare za su tashi a cikin masu kololuwar daraja a Aljannah.”

Kara karanta wannan

Yadda Na Tsallake Rijiya Da Baya a Harin Da Boko Haram Suka Kai Masallacin Juma'a a Kano, Farfesa Sani Zahradeen

Amin.

Ana yi wa Liman kyakkyawan zato

Aliyu Abubakar Zazzau wani abokin Marigayin ne, wanda ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa. Zazzau ya ce Alaranman ya rasu ne ya limancin sallar dare.

Amal Abubakar yake cewa ya samu labarin rasuwan malamin a cikin wannan wata mai alfarma. Amal ya ce irin wannan karshe na Sani Lawal abin madalla ne.

A halin yanzu jama’a su na ta aika sakon ta’aziyyarsu ga ‘yanuwansa da dalibansa da daukacin mutanen Unguwar Samaru, tare da rokon samun irin cikawarsa.

Watan Ramadan shi ne watan da ya fi kowane daraja da falala a addinin musulunci. Sannan kuma dare musamman irin na jiya yana daga cikin mafi daraja.

Sarkin Waka v Nafisa

A ranar Juma'a, Naziru M. Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya soki masu sana’ar wasan kwaikwayo, a kokarinsa na kare Almajirai a Arewacin Najeriya.

Sarkin Waka ya nuna babu manyan Almajirai irin ‘yan wasan fim domin su ne asalin mutanen da iyayensu suka fita daga harkarsu, hakan ya jawo wasu martanin.

Kara karanta wannan

A Ranar Aure, Ango ya Fasa Bayan Gano Amarya ta Kaiwa Tsohon Saurayinta Ziyarar Bankwana

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng