Dirama ta ɓarke a Kotu yayin da Matar Aure ta yi ikirarin mijinta ya danna mata saki uku a waya
- Wata Kotu dake zaune a Jos ta rushe auren Ibrahim Ya'u da Amaryarsa Halima Abubakar bayan matar tace mijin ya sake ta ta Waya
- Alkalin Kotun ya karbi shawarar wakilan Mata da Mijinta, inda ya raba auren tare da umarnin Amarya ta biya Angonta sadakin da ya biya
- Mijin ya bukaci Matar ta biya shi harda kudin hidimar da ya mata kafin aure, amma alkali yace ai shima ya amfana bayan aure
Jos, jihar Plateau - Wata kotu dake zamanta a Jos babban birnin jihar Filato, ta datse igiyoyin aure tsakanin Ibrahim Ya’u da matarsa Halima Abubakar.
Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan matar ta yi ikirarin cewa maigidanta ya kirata a wayar salula kuma ya sanar da ita ya sake ta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Halima Abubakar ta shaida wa kotu cewa Mijinta ya danna mata saki a wayar Salula, dan haka ba zata koma gidansa da sunan Aure ba.
Ta kuma yi bayanin cewa ta kira shi a waya, ya sanya ta a amsa kuwwa kuma akwai wasu mata a tare da shi, lokacin ya furta mata kalmar saki.
Shin mijin ya aikata haka?
A nasa bangaren Ibrahim Ya'u ya musanta ikirarin da matarsa ta yi, tare da jaddada cewa idan tana son saki ne ta dawo masa da sadakin da ya biya
Sannan kuma Mijin ya bukaci ta biya dukkan sauran kayayyakin da ya siya mata kafin su yi aure.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Alƙalin kotun, mai shari'a Ghazali Adam, ya ce duba da matakin da wakilan kowane ɓangare suka ɗauka na raba auren da kuma abin da Shari'a ta tanazar, Kotu ta warware auren.
Alƙalin ya yanke hukuncin cewa Amarya zata biya dubu N60,000 kudin sadaki saboda bata kawo shaidar wayar da suka yi ba, wanda zai tabbatar da abin da ta faɗa da baki.
Game da Mijinta kuma wanda ya bukaci ta biya shi N200,000, Alƙalin ya ce:
"Hakan ba zai yuwu ba saboda abin da ya siya mata kafin aure kyauta ce ta soyayya da kuma amincewarta, kuma ya amfana da ita bayan sun yi aure, dan haka sadaki kaɗai zata ba shi."
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin kasa ta haramtawa ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman jima'i a wurin aiki
Kasar Mexico ta hana ma'aikatan dake karkashinta aikata wani abu da ya shafi Jima'i kamar rungumar juna da sumbatar juna a wurin aiki.
Wannan na kunshe ne a wasu sabbin dokokin da gwamnati ta fitar a hukumance ranar Talata, 8 ga watan Fabarairu 2022.
Asali: Legit.ng