Barka: Ministan Najeriya da ya tafi karo ilmi ya kammala Digir-gir a Jami’ar Birtaniya

Barka: Ministan Najeriya da ya tafi karo ilmi ya kammala Digir-gir a Jami’ar Birtaniya

  • Ministan harkokin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ya kammala digiri na biyu da yake yi a ketare
  • Sanata Hadi Sirika yana karatun M.Sc dinsa a jami’ar City University da ke Landan, a kasar Ingila
  • Annobar COVID-19 ta nemi ta kawo cikas a wajen karatun, amma an yaye su Sirika a makon nan

UK - Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter a watan Maris a 2021, Hadi Sirika ya kare kundin binciken da ya rubuta a gaban malaman jami’a.

Hadi Sirika yana karatun digiri na M.Sc a jami’ar City University da ke Landan, kasar Ingila.

Paul Clark shi ne malamin da ya duba binciken da Ministan Najeriyar ya yi a kan samun hadin-kai tsakanin kasashen Afrika a harkar kula da jiragen sama.

Taken Nazari da binciken da Sirika ya yi shi ne "The development of Airline traffic in Nigeria and the relevance of single African Air transport market (SAATM).”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Wannan kundi yana kunshe da kalmomi 12, 000, da shi aka yi la’akari aka ba Ministan digirin M.Sc. Jaridar Katsina Post ta tabbatar da wannan a rahotonta.

Allah ya yi

Bayan kusan shekara da kare kundin da ya rubuta, jami’ar ta Landan ta shirya bikin yaye Sanata Hadi Sirika da sauran daliban da suka kammala Digirinsu.

Ministan Najeriya
Ministan jiragen sama, Hadi Sirika Hoto: @hadisirika
Asali: Twitter

A sakamakon annobar COVID-19, ba a bada dama mutane da yawa su halarci wannan biki domin su taya murna ba, sai dai aka yi abin a makon nan a salin-alin.

A cewar Mai girma Ministan tarayyar, annobar cutar ce ta hana a yaye su tun kafin shekarar nan.

Za a ga bidiyon Sanata Sirika da alkyabba yayin da ake gabatar masa da shaidar karatun digirgir a bangaren kula da harkokin jiragen sama a wannan makaranta.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

An taya shi murna

Mutane a shafukan Twitter su na taya Ministan murnar wannan karin ilmi da ya samu.

“Mu na taya ka murna Ran ka ya dade. Allah ya yi wa satifiket din da ilmin da aka samu albarka, ya sa su taimaki kasar mu. Mu na addu’a gaba ta fi baya kyau.”

- Sulaiman Magaji

"Barka ga jajirtaccen Ministan jiragen samanmu da ya kammala digirin M.Sc a jami’ar City University, London. Wannan karin matsayi da aka samu zai taimaki kasarmu. Barka ‘yallabai!”

- Yusuf Anas

"Barka dai ‘Yallabai! Kusan za a ce ba a taba yin Ministan harkokin jirgin sama irinka ba a Najeriya. Ka kawo sauyi a harkar jirgin sama da gine-gine, habaka aiki a filayen jirgi da farfado da kamfanin jirgin Najeriya.”

- Sulaiman Towalawi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel