Yadda na je kasar waje domin sayowa Kachalla makamin N28.5m inji Yaron Turji
- Musa Kamarawa ya tonawa kansa asiri bayan da ya shiga hannun jami’an ‘yan sandan Najeriya
- Wannan mutumi ya fadi yadda ya je har kasashen waje domin sayowa Halilu Kachalla makami
- Kamarawa wanda ya je har jami’a ya ce yanzu yana da nadamar abubuwan da ya rika aikatawa
Sokoto - Musa Kamarawa wanda ake zargin ya na taimakawa ‘yan bindiga da makamai ya bada labarin yadda ya sayawa Halilu Kachalla wata bindiga.
Musa Kamarawa wanda ya yi karatun boko, har ya samu shaidar Digiri ya shiga harkar fashin daji tun 2018, shekarunsa fiye da uku yana wannan ta’adin.
Jaridar 21st Century Chronicle ta kawo wannan rahoto a ranar Litinin, 31 ga watan Junairu 2022.
Kamarawa ya bayyana wannan da bakinsa a lokacin da wani Mataimakin Sufeta-Janar na ‘yan sanda, Zaki Ahmed ya gabatar da shi ga Duniya a Sokoto.

Kara karanta wannan
Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu
Zaki Ahmed ya ce wannan Bawan Allah, Musa Kamarawa na-kusa ne ga Bello Turji, sannan yana da dangantaka da wasu gawurtattun ‘yan bindigan yankin.

Source: UGC
Rahoton ya ce akwai lokacin da Kamarawa ya je har garin Cotonou a kasar Benin, ya sayowa Kachalla katuwar bindiga da ake daurawa a jikin mota.
A cewarsa, yanzu ya yi da-na-sani, yana mai nadamar wannan danyen aiki da ya aikata a baya.
“Da na je sai na samu motar (makamin) ba ta nan, sai mu ka kira wani dillali a Libya, ya hada mu da wani mutumi a Nijar da ya karbi kudi, ya kawo mana motar.”
“’Danuwa na Aminu ne ya kai wa Kachalla wannan motar. Mun saye ta ne a kan N28.5m.”
“Ina nadamar yin wannan. Na yi alkawari ba zan sake yi ba, kuma zan taimakawa jami’an tsaro wajen cafke ‘yan bindiga a jihar nan.” - Musa Kamarawa.
DIG Zaki ya ce jami’an ‘yan sanda za su cigaba da kokari har sai an karbe wannan makami.
An damke yaran Turji
A makon nan ne ake samu labari daga bakin wannan babban jami’an tsaro a game da galabar da dakarun ‘yan sanda suka yi a kan wasu mutanen Bello Tuji.
An samu shanu 150, bindigogin AK-47 da harsasashi 2,700 da wasu makamai a hannun wadannan ‘yan bindiga da masu taimaka masu a jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng
