Hanifa: Sanusi II, manyan malamai sun yi kalamai masu zafi a kan wanda ya yi kisan gilla
- Kisan Hanifa Abubakar ya jawo mutane da-dama sun fito su na ta yin Allah wadai da wannan danyen aikin
- Hanifa Abubakar mai shekara 5 a Duniya ta gamu da ajalinta a hannun wani malaminta, Abdulmalik Tanko
- Manyan malamai da manyan kasa sun yi kira ga hukuma ta hukunta Tanko domin ya zama darasi ga ‘yan baya
Kano - Daga cikin wadanda suka soki kisan gillar da Abdulmalik Tanko ya yi wa Hanifa Abubakar, akwai manyan malaman addinin musulunci.
Shehunan malamai irinsu Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu sun yi kira na musamman a game da abin da ya faru a hudubar Juma’ar da suka yi.
A hudubarsa ta ranar Juma’a 21 ga watan Junairu 2022 a Dorayi, Sani Umar Rijiyar Lemu, ya soki ja’irin da ya yi wannan aiki, ya kuma yi kira ga hukuma.
Shehin ya bukaci Alkalai su hukunta wannan malamin makaranta tun da har ya amsa laifinsa, ya ce a baya an yi irin haka, amma ba a dauki mataki ba.
Dr. Abdullahi Umar Gadon-Kaya ya yi kira ga hukuma ta kashe Tanko kamar yadda ya kashe Hanifa ta hanyar datsa shi ba tare da wani bata lokaci ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanusi II ya yi jawabi
Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II ya fito ya yi magana, ya ce abin da ya dace shi ne a gaggauta daukan mataki a kan wannan mugun mutum.
Legit.ng Hausa ta samu takaitaccen jawabin da Khalifa Muhammad Sanusi II ya yi a shafin Twitter.
“Wanda ya aikata ya fito ya fada, wadanda ya sa su haka masa rami, sun fito sun fada sun ce shi ya ce su haka masa rami.”
“Idan dai akwai adalci a Nigeria, ya kamata a cikin ‘dan gajeren Lokaci mu ga hukuncin da aka yiwa wannan mutumin.”
“Babu zancen an je kotu, lauya ya yi magana an kara shekara daya…” - Muhammad Sanusi II.
Shi ma Dr. Rabiu Rijiyar Lemu ya fadakar da al’umma a kan kisan gillar da aka yi wa wannan karamar yarinya, ya ce dole a fito fili a hukunta mai laifin.
Da yake gabatar da lacca a masallacin ITN Zaria, Sheikh Nura Zubairu Dambo ya yi irin wannan kira.
Aisha Buhari ta goyi-baya
Uwargidar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta nuna goyon bayanta kan kiran da ake yi na cewa a hukunta malamin da ya hallaka Hanifa Abubakar.
Mai dakin Mai girma Muhammadu Buhari tana goyon bayan hukuncin da Shiekh Abdallah Gadon Ƙaya ya nema a yanke wa wannan mutumi mai shekara 35.
Asali: Legit.ng