Shugaban BUA ya samu kusan rabin Tiriliyan a kwana 7 a lokacin da Dangote ya yi asara

Shugaban BUA ya samu kusan rabin Tiriliyan a kwana 7 a lokacin da Dangote ya yi asara

  • Tseren da ake yi tsakanin Attajiran kasar nan ya na kara ban kayi a farkon shekarar nan ta 2022
  • Na biyu a jerin masu kudin kasar, Abdulsamad Rabiu ya samu N420bn a dukiyarsa a mako guda
  • Dukiyar shugaban kamfanin na BUA ya karu ne a lokacin da aka ji Dangote ya rasa kusan $200m

Abubuwa su na ta kara yi wa babban attajirin nan, Alhaji Abdulsamad Rabiu kyau a sabuwar shekarar ta 2022 da aka shiga makonni biyu da suka wuce.

Rahotanni sun tabbatar da cewa arzikin Abdulsamad Rabiu ya karu a kwanaki 15 da suka wuce.

Bayan ya doke Mike Adenuga, ya zama mutum na biyu da ya fi arziki a Najeriya, shugaban kamfanin na BUA ya samu karin N420bn a cikin mako daya.

Wani rahoto da ya fito daga Nairametrics ya bayyana cewa Rabiu ya yi gaba ne bayan darajar kamfaninsa ya karu da 65% bayan ya sa hannun jari a kasuwa.

Kara karanta wannan

COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a shekara 2

Darajar kamfanin da Alhaji Abdussamad Rabiu ya bude a shekarun baya ya zarce Naira tiriliyan 1. A makon da ya wuce, an yi wa BUA daraja ne da kusan N650bn.

Shugaban BUA da Dangote
Dantata, Ganduje, Dangote, da BUA Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

#2 a Najeriya, #6 a Afrika

Kamar yadda Forbes ta bayyana, Abdulsamad Rabiu ya mallaki kusan Dala biliyan biyar. Hakan na nufin shi ne na 584 a masu kudin Duniya, na shida a Afrika.

Dukiyar attajirin za ta cigaba da karuwa idan hannun jarin kamfanoninsa suka cigaba da kara daraja.

Alhaji Rabiu da ‘dansa ne suke da kusan 98% na hannun jarin kamfanin simintin nan na BUA cement. Shi ma wannan kamfani ya na da kusan Naira tiriliyan biyu.

Dangote ya yi asarar N80bn

Ko da Aliko Dangote shi ne babban mai kudin Najeriya da kaf nahiyar Afrika har yanzu, sai dai ya yi asarar Dala miliyan $194 (Naira biliyan 80.37) a shekarar bana.

Kara karanta wannan

Kamar wasa: Yadda matashi ya sayar da hotunansa na selfie kan kudi N415m

Duk da asarar da Dangote ya tafka a karshen makon da ya wuce, alkaluman Bloomberg index sun nuna attajirin ya mallaki kusan Dala miliyan 20, kuma bai da sa’a.

Abdul Samad Rabiu ya zabura

A makon jiya ne rahotanni suka tabbatar da cewa cewa Alhaji Abdul Samad Rabiu ya zama na biyu yanzu a jerin masu kudin kasar nan, ya na bayan Aliko Dangote.

Rabiu ya mallaki sama da Dala biliyan 7 a halin yanzu. A lissafin Legit.ng Hausa, kusan Naira tiriliyan 3 kenan Attajirin da ya kafa kamfanin BUA ya ba baya a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng