COVID-19 ta azurta Attajiran Najeriya 3, sun samu karin Naira Tiriliyan 3 a cikin shekara 2
- Binciken The Oxfam in Nigeria ya nuna yadda dukiyar masu kudi ta nunku a annobar COVID-19
- Masu kudin kasar nan sun samu karin akalla Naira Tiriliyan 2.895 a dukiyarsu cikin shekaru biyu
- A daidai wannan lokaci kuma talakawa sun kara yawa, mafi yawan mutane sun shiga halin ha’ula’i
FCT, Abuja - Kamfanin Oxfam ya bayyana cewa daga watan Maris a 2020, dukiyar wasu manyan masu kudin kasar nan ta karu da kimanin fam Dala biliyan 6.9.
Daily Trust ta ce arzikin wadannan Attajirai uku ya karu ne a daidai lokacin da sauran al’umma suka kara shiga halin ni – ‘ya su a lokacin annobar cutar COVID-19.
Cikakken bayanin nan ya zo ne a wani rahoto mai taken: “Inequality Kills” -The unparallel action needed to combat unprecedented inequality in the wake of COVID-19.
Wannan rahoto mai shafi 59 da aka fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Junairu, 2022 a garin Abuja ya nuna irin shan bam-ban da ake samu tsakanin talaka da mai hali.
Shugaban kungiyar nan ta CISLAC watau Auwal Musa Rafsanjani da takwarorinsa na Oxfam in Nigeria; Henry Ushie da Chinedu Bassey suka kaddamar da rahoton.
Mutum 2 sun dama miliyan 60
Kamar yadda jaridar ta fitar da labarin, Dr. Vincent Ahonsi ya ce abin takaici ne yadda arzikin manyan Attajirai biyu a Najeriya, ya zarce na talakawa miliyan 63.
Darektar kungiyar Gabriela Bucher ta ce dukiyar mashahuran Attajiran Najeriya ta karu da 38%, yayin da mutum miliyan 7.4 suka zama talaka tubus a shekarar 2020.
Mutane 4,690 ne suke da akalla Dala miliyan biyar a Najeriya. Sannan kuma akwai masu kudi 245 da abin da suka mallaka ya haura $50m, gaba daya dai sun tara $56.5bn.
Masu kudi sun kara kudi, talaka sun kara tsiyacewa
Wannan rahoto na Oxfam in Nigeria ya nuna arzikin manyan masu kudin Duniya ya nunku fiye da sau biyu a wadannan shekaru da ake fama da annobar Coronavirus.
Daga $700bn, Attajirai goman farko da ake ji da su a fadin Duniya sun ba $1.5trn baya a yau. Hakan ya nuna nufin sun samu $1.3bn a duk rana daga 2020 har zuwa yanzu.
Su kuma talakawa sun kara shiga cikin tasko ne a halin yanzu. Mutane miliyan 160 suka zama talaka a wannan marra bayan sun rasa 99% na duk abin da suka mallaka.
TSA bai hana komai ba
Ku na da labari cewa tun a shekarar 206 ne Gwamnatin Muhammau Buhari ta dabbaka tsarin TSA da nufin rage sata a gwamnati da tabbatar da gaskiya a wajen aiki.
Shekaru shida da kawo wannan tsari, bincike ya nuna har yanzu ma’aikatan su na yin satarsu.
Asali: Legit.ng